Xender manhajar ce da muka fi sani wajen yin aikawa da karbar sako wato ‘transfer’ na ‘files’ (bideos, audios, photos, applications da sauransu) daga wata wayar zuwa wata waya daban.
A tsakanin Android da Android, ko Android da iPhone, ko tsakanin Androi da Kai OS, ko kuma tsakanin waya da computer.
- Nijeriya Ta Yi Barazanar Ficewa Daga Kungiyar ECOWAS
- Kotu Ta Raba Auren Wanda Ya Auri Jikarsa A Zamfara
Akwai kuma wasu muhimman aiyuka da za mu iya yi da dender wandanda suka hada da:
1. Sauke status na WhatsApp
2. Sauke ‘bideo’ daga Facebook, Twitter da Instagram
3. Conberting na ‘bideo’ zuwa ‘Audio’
4. Mayar da kayan (files) na tsohuwar waya zuwa sabuwar waya (cloning)
Yadda Ake Sauke Status (Video ko Photo) daga WhatsApp Kafin ka sauke ‘status’ na WhatsApp ta hanyar amfani da dender, sai ka bude (status biewing) ta WhatsApp da farko tukunna, sai ka shiga cikin dender, ka duba can kasa, za ka ga ‘social’, sai ka shiga ‘social’.
Duk ‘status’ din da ka bude za su fito a nan, sai ka zaba, ka yi ‘sabing.’
Yadda Ake Sauke Video Daga Facebook, Twitter Da Instagram Idan kana bukatar sauke (downloading) na wani ‘bideo’ daga Facebook, Twitter ko Instagram ta hanyar amfani da dender ga matakan da zaka bi:
• Za ka yi ‘copy’ na link din wannan bideon.
• Sai ka bude xender, ka shiga wannan wajen na ‘SOCIAL’
• Sai ka shiga wajen da aka rubuta ‘PASTE AND DOWNLOAD’, sai ka
bude, ka yi ‘paste’ na wancan link da ka yi copied din. Wato ka danne ya tsanka a wajen, za ka ga link din ya sauka.
• Zai yi ‘analyzing’ na link din na lokaci kadan, sai kuma ya fara sauka (downloading).
Yadda Ake Mayar Da Video Zuwa Audio
(Conberting) A Xender Ana iya amfani da Xender wajen mayar da bideo na kallo, zuwa audio na saurare. Wato ‘conberting’ na ‘bideo’ ya koma ‘audio’ ta wadannan matakan:
• Ka shiga cikin ‘Xender’
• Ka duba daga kasa, za ka ga wani waje ‘bottom’ an rubuta ‘ToMp3’, sai ka shiga ciki.
• A ciki, zai baka zabi guda biyu.
Na farko, ToMp3, na biyu kuma LOCAL.
Za ka iya shiga ta kowannensu, don nemo ko zabar bideon da kake son mayar wa Mp3 din (audio).
Mayar Da Kayan (Files) Na Tsohuwar
Wayarka Zuwa Sabuwar Waya Idan ka canza wayarka, wato ka sayi sabuwar waya, kuma kana so ka ka kwashe abubuwan ka na kan tsohuwar wayar taka, to ana amfani da Xender cikin sauki wajen kwashe su.
Xender tana da tsarin CLONE, tsari ne da zai baka damar ‘transfer’ na ‘files’, applications, contacts da sauransu, daga wata wayar zuwa wata wayar.
Wannan tsarin na CLONE zai ba ka amar debe kayan tsohuwar wayarka, zuwa sabuwa ba tare da ka rasa komai ba, ciki har da ‘messages’ da ‘call history’.
Yadda zaka yi amfani da wannan tsarin na ZENDER CLONE shi ne:
• Ka duba cikin Zender da kyau, daga can sama (bangaren dama) akwai wasu digo guda uku, icon ≡, sai ka shige shi.
• A menu din, ka duba na karshe, shi ne ‘phone cooy’, sai ka shige shi.
• Sai ka zaba a cikin wayoyin biyu, daya NEW (wacce za a turawa), daya kuma OLD (wacce za ta tura din).