Hausawa kan ce “duniya juyi-juyi ne “. To, yau za mu tattauna batun da ya shafi juyi-juyi, ko kuma sauyin, da ke faruwa a duniya.
Yanzu haka ana iya ganin sauyawar yanayi dangane da kasar Amurka: Bayan da shugaba Donald Trump ya koma fadar shugabancin kasar Amurka ta White House, kasar ta riga ta janye jiki daga hukumomin kasa da kasa da suka hada da majalisar kare hakkin dan Adam dake karkashin Majalisar Dinkin Duniya, da hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, da yarjeniyoyin da suka hada da yarjejeniyar tinkarar sauyin yanayi ta Paris, da ta tsara ayyukan tinkarar sauyin yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya, ta yadda kasar ta yi watsi da nauyin dake wuyanta a cikin wadannan hukumomi da yarjeniyoyin kasa da kasa. Ban da haka, matakan da Amurka din ta dauka a cikin gida na korar da ‘yan kasashen waje, da rufe hukumar raya kasa da kasa ta Amurka ta USAID suna mummunan tasiri kan kasashen Afirka. Idan mun dauki kasar Najeriya a matsayin misali, za mu ga yadda aka tsare ‘yan Najeriya fiye da dubu 200 a kasar Amurka, wadanda za a iya maida su gida. Kana dakatar da aikin USAID ita ma ta haddasa gibin kudin da ake bukata wajen gudanar da ayyukan tinkarar cutar kanjamau, da ta tibi, da ta zazzabin cizon sauro, a kasar ta Najeriya.
- Mutane Da Dama Sun Jikkata Sakamakon Fashewar Wani Abu A Kasuwar Zamfara
- Gwamnatin Kebbi Ta Samar Da Tirela 300 Na Abinci Don Rabo Da Azumi
Sai dai sauyawar manufofi ba ta nufin canzawar halayyar kasar Amurka. Hakika yadda Amurka din ta yi fatali da nauyinta a cikin hukumomin kasa da kasa, da aikin kulawa da ‘yan kasashen waje, da tallafin da take samar wa sauran kasashe, ya nuna cewa, kasar sam ba ta canza manufarta ta daukar matakan kashin kai ba. Dangane da batun, jaridar Daily Trust ta kasar Najeriya ta ce abun da kasar Amurka ta yi, shi ne cire “rigarta” ta karamci. Yayin da a nata bangare, jaridar The Independent ta kasar Uganda ta ce yadda aka rufe hukumar USAID yana da kyau, saboda kasar Amurka ta dade tana amfani da hukumar wajen bayyana kanta a matsayin wata kasa “mai tausayi”, inda aka rubuta cewa, “Kasar Amurka ta ware dala kusan biliyan 900 duk shekara ga bangaren aikin soja, don jefa boma-bomai da kashe fararen hula a wurare daban daban, yayin da a nata bangaren hukumar USAID ta kashe dala biliyan 40 a kowace shekara, sa’an nan ta sanya mutane da yawa amincewa da matsayin kasar Amurka na ‘mai tausayi’.” To, daga yin kisa yadda ta ga dama, da neman samun fin karfi da yin babakere, zuwa yin fatali da nauyin dake wuyanta, da mai da moriyar kasar Amurka gaban ta sauran kasashe, anya ana iya ganin sauyawar halayyar kasar Amurka a ciki? A ‘a, sam ba za a gani ba.
Saboda haka, ya kamata kasashe masu tasowa su dauki matakai don tinkarar manufofin kasar Amurka na kashin kai, wadanda ba za ta taba canzawa ba, maimakon mai da hankali kan wasu manufofin kasar na gajeren lokaci, wadanda ke sauyawa har kullum. Amma ta yaya za a iya tinkarar manufar kasar ta kashin kai? Shawara daga kasar Sin ita ce, a dauki manufar cudanyar sassa daban daban.
Ma’anar manufar ita ce, a yi kokarin samar da dabarar daidaita al’amura ta hanyar tattaunawa. Kana bangarori daban daban su samu damar tsara ka’idoji, wadanda za a bi su tare. Ban da haka, bai kamata a ba kasashe kalilan ikon tillastawa sauran kasashe wasu ka’idoji, ko kuma ba wasu kasashe masu karfi ikon ba da umarni ba. Tsakanin manufar nan da ta kashin kai, za a ga wata na dora muhimmanci kan hadin kai, yayin da wata ke daukaka fin karfi da ja-in-ja. Saboda haka cikin sauki za a iya bambance su, da ganin wanne ne daga cikinsu ya fi nuna yanayi na adalci.
Ban da haka, idan mun mai da hankali kan cudanyar kasashe daban daban, da zamansu tare a cikin duniya, za mu san huldar da ake da ita tare da Amurka, wani bangare ne kawai na huldar kasa da kasa. Saboda haka, yayin da wata kasa ta gamu da matsala, idan wata kasa ta nade hannu, ba ta son ba da taimako, tabbas ba za a rasa bangarorin da ke son samar da taimakon ba. Matukar an yi kokarin kulla abokantaka bisa ra’ayi na daidaiwa daida, da amfanawa kowa, to, tabbas ba za a rasa abokin hulda ba.
Sai dai idan mun nazarci sabbin matakan gwamnatin kasar Amurka, za mu ga kusan dukkansu na da nufin tsimin kudi da tabbatar da karin kudin shiga, inda ake iya ganin alamar sauyawar matsayin kasar daga mai cikakken yakini zuwa mai ra’ayin rikau, har ma ta yi watsi da kimarta da kwarjininta. Dalilin da ya sa Amurka yin haka, shi ne, ci gaban kasashe masu tasowa bisa hadin gwiwarsu na haifar da ainihin sauyawar yanayi ga tsare-tsaren kasa da kasa. (Bello Wang)