Rabiu Ali Indabawa
Majalisar Dattawn Amurka na ci gaba da binciken zargin da take yi wa Rasha cewa ta yi wa zaɓen Amurka na shekarar 2016 shishshigi da nufin karkata tunanin masu zaɓe.
Kwamitin tattara bayanan sirri na Majalisar Dattawan Amurka ya bayyana cewa zai ci gaba da bincikensa don gano ko kwamitin kamfen ɗin shugaban ƙasa Donald Trump ya haɗa kai da ƙasar Rasha wajen sauya alƙiblar zaɓen Amurka na shekarar 2016, yayin da ke gargaɗin cewa katsalandan ɗin Rashar zai iya ci gaba ya kuma zamo barazana ga zaɓuɓɓuka masu zuwa.
Shugaban kwamitin,Richard Burr ɗan jam’iyyar Republican daga jihar North Carolina, ya ce, “Har yanzu maganar katsalandan ɗin zaɓen tana nan.”
Yawancin manyan jami’an harkokin tsaron ƙasa na Trump sun amince da sakamakon da kwamitin tattara bayanan sirri na Majalisar Dattawan ya samu, na cewa Rasha ta yi katsalandan a zaɓen shekarar da ta gabata, ta kuma taimakawa Trump a zaben.