A cikin hawayen kuka ne da jimami aka bizne Sarkin Adara, Dakta Galadima Maiwada, wanda wasu da ake kyautata zaton masu satan mutane ne suka kashe makwanni biyu da suka wuce, an bizne shi ne a garin Kaciya, ta karamar hukumar ta Kaciya, Jihar Kaduna, a ranar Asabar.
Kisan na Sarakin na Adara, bayan da aka biya wadanda suka sace shi din kudin fansa Naira Milyan 6.8 daga cikin Naira milyan 100 da suka nema, ya kunna wutar wani rikicin a Jihar, wanda ya tilasta wa Gwamnatin Jihar kakaba dokar hana fita ta dindindin.
An bizne Basaraken ne a cikin tsattsauran matakan tsaron da ba a saba gani ba, a wurin da aka saba bizne Sarakunan yankin da ke garin na Kaciya.
A wajen jana’izan wacce aka yi a Cocin Katolika, na garin na Kaciya, Bishop din Cocin na yankin Kaduna, Rabaran Matthew Ndagoso, ya yi gargadi kan furta kalaman da ba su dace ba daga bakunan shugabannin siyasa, yana mai cewa, kamata ya yi gwamnati ta kasance mai yin adalci ga kowa.
Limamin Cocin ya ce, rigingimun da ake fama da su a kasar nan, ba ana yi ne a tsakanin mabiya manyan Addinan nan guda biyu ba, Kiristoci da Musulmai, ana yi ne a tsakanin masu tsattsauran ra’ayi, masu satan mutane da ‘yan ta’adda.
Domin a cewar sa, mabiya Addinan biyu ai ba sa yakan junan su, ya ce, kamata ya yi masu mulki su nemo masu aikata laifukan a cikin kasar nan.
Malamin na Cocin ya ce, “In har ana son samar da tabbataccen zaman lafiya mai dorewa a cikin kasar nan, dole ne a yi aiki da wadannan matakan, kamar na nuna bambanci wajen rabon tattalin arzikin kasa, take hakkin dan adam, fitar da tsare-tsaren da suke nuna son kai da rashin adalci.
Ya kuma yaba wa hukumomin tsaro a bisa kokarin da suka yi na tabbatar da zaman lafiya a cikin Jihar, ya kuma yi kira ga gwamnati da ta kara zuba jari sosai a kan sashen na samar da tsaro.