Ana zargin wani mutum mai suna Dauda Bello, mai kimanin shekara 54 da laifin kashe wata tsohuwa mai suna Misis Mesesi Adisa da sayar da sassan jikinta.
Majiyarmu ta shaida mana cewa, bayan kama wanda ake zargin, ranar 7, ga watan Yuli, ya tabbatar wa da ‘yansanda,yadda ya kashe wannan tsoho, ya kuma sayar da kafadunsa da kuma kafafunsa. Marigayiyar Misis Adisa ta bata bat ne jim kadan bayan fitowarta daga gida.
Bayan faruwar wannan lamari ‘yan’uwan marigayiyar sun kai rahoto ofishin ‘yansanda na Sabo/Ilupeju, daga baya kuma suka koma ofishin masu yaki da masu garkuwa da ke sashin binciken manyan laifuka.
SP Taiwo wanda ke gudanar da bincike kan wannan lamari, ya ce guri na karshe da marigayiyar ta je shi ne, gidan wanda ake zargi da ke yankin Olodo a Abeokuta ta Arewa cikin jihar Ogun.
Mai Magana da yawun rundunar ‘yansanda na jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi,ya ce an tsare wanda ake zargin a ofishin ‘yansanda, domin ci gaba da gudanar da bincike.
Binciken da muka fara, wanda ake zargin ya tabbatar da cewa, sun dade suna sayar da mutane. Ya kara da cewa shi ne ya kira marigayiyar zuwa gidansa, domin su tattauna kan kasuwancinsu na sayar da mutane, sai lokacin da suke gana wa a gidansa, ya fahimci cewa,ta zo da wasu kudi masu yawa.
Wannan ta sa, ya kai mata duka a ka da wani katon katako, wanda kuma nan take ta fadi kasa sumammiya, ganin cewa ta mutu, sai ya dauki gawar ya kai ta daji.
Oyeyemi ya ce, wanda ake zargin ya tabbatar da aikata laifin, bayan kashe matar ya kuma lalube ta, wanda ya samu naira 22,200 a wajenta, bayan wannan danyen aiki sai ya gudu.
Da ya yi tunanin zai samu kudi masu yawa a wajen wannan tsohuwa,amma sai ya ga babu kudin da yake tsammani.
A kaeshe, wanda aka kaman ya kai ‘yansanda dajin da ya binne gawar wannan mata, sannan kuma ya nuna wa ‘yansanda wasu sassan jikin matar da ya cire.
Kwamishinan ‘yansanda, Lanre Bankole, ya umarci a gaggauta gurfanar da wanda ake zargin gaban kotu, domin yi masa hukunci.