An ciro wata mata da rai bayan ta makale a cikin baraguzan ginin da ya ruguje sa’o’i 52 sakamakon wata mummunar girgizar kasa da ta auku a Kudu Maso Gabashin Turkiyya.
Hotunan gidan talabijin na NTV a ranar Laraba sun nuna ayyukan agajin gaggawa a lardin KahramanmaraÅŸ da ke kusa da kan iyaka da Siriya dauke da matar a kan gadon asibiti zuwa motar daukar marasa lafiya.
- Kotun Koli Ta Dakatar Da Daina Amfani Da Tsofaffin Kudi Na Wucin Gadi
- Jami’in DSS Na Bogi Da Wasu Sun Shiga Hannu A Osun
An ce an kubutar da matar mai shekaru 58 a wani otal da ya ruguje.
Lardin KahramanmaraÅŸ ya fuskanci girgizar kasa mafi muni.
Girgizar kasar ita ce mafi karfi wacce ta kai ma’aunin mita 7.7 kuma ta auku da karfe 01:17 agogon GMT a ranar Litinin.
Wata girgizar kasa mai karfin gaske, wacce ta dan yi rauni da karfe 7:5, ta auku da tsakar rana a wannan rana.
Dubban mutane ne suka mutu a Turkiyya da makwabciyarta Siriya.
Kamfanin Dillancin Labaran Iqna, ya bayyana cewa, an kai wasu daga cikin wadanda suka jikkata zuwa babban birnin Istanbul domin yi musu magani ta filin jirgin saman Atatürk, wanda aka rufe don zirga-zirgar jiragen sama.