An Daina Fashin Zuwa Aiki A Karamar Hukumar Kunchi – Shuwaki

Daga Abdullahi Muhammad Sheka,

Shugaban Karamar Hukumar Kunchi Alhaji Aminu Idi Shuwaki, ya bayyana kudirinsa na cewa batun fashin zuwa aiki a Karamar Hukumar Kunchi daga wannan rana ya zama tarihi, domin kuwa a cewar tasa, ba zai dagawa kowa kafa a wannan lokaci ba. Ya kara da cewa, duk wanda ya zabi fashin zuwa aiki, ko shakka babu zai sanya kafar wando guda da shi. Shugaban ya bayyana haka ne a ranar Larabar da ta gabata, jim kadan bayan rantsar da Kansiloli goma na Karamar Hukumar ta Kunchi, wanda aka gudanar a Sakatariyar Karamar Hukumar.

 

Alhaji Aminu Shuwaki ya ci gaba da cewa, “ina son tabbatarwa da kowa da kowa tun daga kan Shugaban Ma’aikata har zuwa kan Masinja cewa, babu wanda zai ci gaba da fashin zuwa aiki na zuba masa ido, daga nan har gaban Gwamnan Jihar Kano, sai na tabbatar da ganin an hukunta duk wani mai kunnen kashi kan aikin da aka damka amanarsa a hannunsa. Saboda haka, ina kira da babbar murya, domin kuwa ba mu da Karamar Hukumar da ta wuce ta Kunchi, don haka dole ne mu zage damtse domin ciyar da yankin da muke alfahari da shi.

 

Da ya waiwayi bangaren ‘yan siyasa, Alhaji Aminu Shuwaki ya tabbatarwa da al’ummar Kunchi cewa, shi bai yarda da siyasar jagaliyanci ba, ma’ana bai yiwuwa ka zo ka yaba masa, kuma ka koma gefe kana zagin wani dan siyasa, ko da kuwa ba jam’iyyarsu guda da shi ba, wanda duk ya aikata haka to kuwa ya sani har kofar gida zan aiki jami’an tsaro su damko shi. “Mu siyasarmu na da kyakkyawar alkibla, alkiblarmu ita ce gaskiya da kishin kasa gami da al’ummarmu baki-daya.”

 

Haka zalika, Shugaban Karamar Hukumar ta Kunchi, ya bukaci Malamai Magada Annabawa da su kara himmatuwa wajen tsayawa tsayin daka wajen fada musu gaskiya, wanda a cewar tasa wannan shi ne gatan da Malamai ya kamata su yi wa duk wani mai mulki. “A shirye nake da karbar duk wata nasiha da kuma shawarwarin iyayen kasa da Malamai, domin fatan Allah Ya inganta jagorancin namu.”

 

Da yake yin jawabi ga Kansilolin da aka rantsar a wannan rana, Alhaji Aminu Idi Shuwaki ya bukace su da su hada kai domin yin aiki tare, kasancewarmu ‘ya’yan wannan Karamar Hukuma, wadda ba mu da wani wuri da ya wuce ta. Saboda haka, sai ya tabbatar masu da cewa an daina gudanar da aiki daga wani wuri, a Karamar Hukuma kowa zai fito a yi aiki da shi, sannan kuma dukkanin wasu kadarorin gwamnati dole ne su dawo aiki ciki a cikin wannan Karamar Hukuma ta Kunchi, domin kadarar al’ummar Kunchi ce. A karshe Shugaban ya yi addu’ar fatan Allah Ya shiga cikin al’amarin wannan sabon Shugabanci.

 

An dai gudanar da wannan bikin rantsar da Kansiloli ne a gaban mai girma Hakimin Kunchi, manyan Daraktocin mulki, Shugabannin sassan mulkin Karamar Hukuma, Jami’in ‘Yan Sanda mai lura da Karamar Hukumar Kunchi, Shugabannin  Jam’iyyar APC da sauran manyan mutane ne suka halarci bikin rantsuwar.

Exit mobile version