• English
  • Business News
Sunday, October 19, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Dakatar Da Bin Uthman Daga Limancin Masallacin Sahaba, DSS Ta Gayyace Shi

by Abubakar Sulaiman
9 months ago
sahaba

Mahukunta a Masallacin Jami’ur Rahman, da aka fi sani da Masjid Sahaba a baya, sun dakatar da Sheikh Muhammad Bin Uthman daga jagorantar sallah da yin huɗuba, bayan wata huɗuba da ya yi a ranar 24 ga Janairu 2025 da ta jawo ce-ce-ku-ce a masallacin.

Sheikh Bin Uthman ya jagoranci tsohon masallacin Sahaba na tsawon shekaru 24 kafin gina sabon masallacin a kusa da shi wanda fitaccen ɗan kasuwar nan AY Maikifi ya gina. Wannan sabon wurin a baya filin shakatawa ne da jama’a ke taruwa don Sallar Juma’a da ta Eid.

  • Bidiyon Dala: Kotu Ta Dakatar Da Gwamnatin Kano Da ‘Ƴansanda Da DSS Kan Kama Ganduje
  • Gwamnatin Sakkwato Za Ta Kashe Miliyan 95.4 Domin Gyara Masallatan Juma’a

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, Malamin a huɗubarsa ta ranar Juma’a 24, ga Janairun 2025, Sheikh Bin Uthman ya bayyana yadda aka ware shi daga jagorantar sabon masallacin, duk da cewa shi ne tsohon limamin masallacin. Ya ce hukumar masallacin ta naɗa ƙarin limamai uku ba tare da yin la’akari da shi ba.

Bayan huɗubarsa, an samu wasu cikin mabiya masallacin sun fusata, har suka kusa kai wa sakataren kwamitin amintattun masallacin, Abdulƙadir Isawa, hari.

A wata wasiƙa da daraktan kula da masallacin ya sanya wa hannu, an sanar da dakatar da Sheikh Bin Uthman har sai an kammala bincike. An kuma buƙace shi da ya miƙa duka wata dukiyar masallacin da ke hannunsa.

LABARAI MASU NASABA

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

A ranar Litinin, hukumar tsaro ta DSS da Majalisar Ulama sun kira Sheikh Bin Uthman da AY Maikifi don tattaunawa da su. A gefe guda kuma Majalisar Ulama ta shawarci Sheikh Bin Uthman da ya koma masallacinsa na asali, amma har yanzu dai ba a san ko zai amince da hakan ba.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus
Manyan Labarai

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya
Da ɗumi-ɗuminsa

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna
Manyan Labarai

Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Ofishin Ƴansanda, Sun Kashe 2 A Kaduna

October 18, 2025
Next Post
katsina

Gwamnatin Katsina Ta Fitar Da Naira Miliyan Dubu 50 Domin Samar Da Ruwan Sha 

LABARAI MASU NASABA

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

An Sanya Hannu Kan Yarjejiyar Zaman Lafiya A Gaza

October 19, 2025
Nijar

Gwamnatin Nijar Ta Yaye Tsofaffin Mayaka 369 Da Aka Bai Wa Horon Sauya Tunani

October 19, 2025
Yadda Zargin Takardar Karatun Bogi Ta Tilasta Wa Minista Nnaji Murabus

‘Yan Siyasa 11 Da Suka Faɗa Dambarwar Takardar Shaidar Karatu Ta Bogi

October 19, 2025
gombe

Ɗaliban Jihar Gombe Sun Samu Ƙarin Kashi 100 Na Kuɗin Tallafin Karatu

October 18, 2025
Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

Ɗaliban Fasaha Sun Ɓullo Da Dabarar Tsaro Ta Harkar Noma

October 18, 2025
An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

An Bude Taron Sanin Makamar Aiki Na Cika Shekaru 80 Da Kafuwar MDD A Wuhan Na Kasar Sin

October 18, 2025
Tsadar Rayuwa Da Karuwar Ta’addanci Na Ci Gaba Da Tagayyara ‘Yan Nijeriya

DHQ Ta Ƙaryata Rahoton Yunƙurin Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

October 18, 2025
Da Ɗumi-ɗumi: ‘Yansanda Sun Tarwatsa Masu Zanga-zangar Adawa Da Dokar Ta-ɓaci A Ribas

‘Yansanda Sun Kai Samame Maboyar ‘Yan Ta’adda, Sun Kwato Miyagun Kwayoyi A Gombe

October 18, 2025
Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

Kamfanin Gine-Gine Na CCECC Ya Fara Gina Wani Titin Mota Da Zai Rage Cunkoso A Birnin Abuja Na Tarayyar Najeriya

October 18, 2025
ASUU

Cikin Wata 9 Farfesoshi 309 Sun Bar Aiki A Jami’o’in Gwamnati, In Ji ASUU

October 18, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.