Alkalan Kotun Majistare uku da aka dakatar kuma aka maida su shelkwatar gidan shari’a a Jihar Kebbi, sun roki hukumar kula da harkokin shari’a ta kasa (NJC) da ta shiga tsakani kan lamarin da ya kai ga dakatar da su saboda nuna sha’awarsu na neman mukamin Alkalin Babbar kotun jihar.
Alkalan da abin ya shafa, wadanda suka bayyana dakatarwar tana a matsayar cin zarafi kuma da bata masu tahirin aiki a gidan shari’a, sun roki NJC da ta taimaka wani bincike da tantance tare da bayyana gaskiyar lamarin kan neman mukamin Alkalin Babbar kotun Jihar da suka yi wanda ya sanya ana yi musu bita da kulli.
- Hanyoyin Kula Da Fatar Jiki (4)
- Jam’iyyar PDP A Kebbi Ta Shirya Tarbar Dan Takarar Shugaban Kasa, Atiku Abubakar
Wakilinmu ya ce wadanda abin ya shafa sun hada da: Babban Majistare Mustapha Umar-Maccido, Babban Kotun Majistare da ke Kalgo, Majistare Umar Salihu-Kokani, Babban Kotun Majistare ta uku da ke Birnin Kebbi da Majistare Halima Umar, Babban Kotun Majistare ta biyu da ke Birnin Kebbi.
Har ila yau, bisa ga rahotanni sun ce an dakatar da Majistare Umar-Maccido ne bisa zarginsa da laifin gujewa daga aiki da gudanar da ayyukan lauyanci a wasu kotutun a wasu jihohin kasar cikin a sirri, an kuma kiran Majistare Salihu-Kokani zuwa hedikwatar gidan Shari’a ta jihar bisa zarginsa da mari wani lauyan gwamnati, Abdullahi Bawa-Dan-Bauchi, wanda solisita janaral ya rubuta korafi akansa.
Haka kuma Majistare Halima Umar itama an yi mata kiraye zuwa hedikwata bisa zarginsa da aikata laifin sakin barayin shanu akan beli.
Idan za a iya tunawa, a ranar 14 ga Oktoba, 2022, babban magatakardar babbar kotun jihar Kebbi, Hussain Abdullahi-Zuru ya sanar da dakatar da Alkalin Mustapha Umar-Maccido da Alkalai Umar-Salihu Kokani ta wata sanarwa da ya sanya wa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Birnin Kebbi.
Da ya ke zantawa da manema labarai a Birnin Kebbi a madadin Alkalan ukun da lamarin ya shafa Majistare Umar-Maccido ya danganta abin da ya faru da su da irin sha’awar da suka nuna a kan mukaman manyan alkalan kotunan shari’a na jihar ta hanyar shigar da takardun su na nuna suna neman zama Babban Alkalan Babbar kotun Jihar watau (High court judges).
Ya ce, an tilasta musu yin magana da ‘yan jarida ne saboda hukumar da abin ya shafa ta yi gaggawar garzayawa kafafen yada labarai don bata musu suna, maimakon a sasanta lamarin cikin ruwan sanyi ta hanyar amfani da hanyoyin da suka dace da doka ta gidan Shari’a idan har neman mukamin Alkalin Babbar kotun Jihar laifi ne, inji shi.
Kazalika ya kara da cewa, “Duk wadannan matsalolin sun samo asali ne sakamakon sha’awar da muka nuna na daukaka matsayin alkalan babbar kotuna jihar. Duk zargin da ake mana ba gaskiya ba ne, inji Majistare Mustapha Umar Maccido”.
“A makon da ya gabata ne aka dakatar da Majistare Halima Umar ta Kotun Majistare ta Biyu da ke Birnin Kebbi, bisa wani batu da ake zargin ta bayar da belin barayin shanu.
“Wannan laifin babban laifi ne wanda ya kai shekaru 14 a gidan yari ba tare da belin ba, wanda ba ta da huruminsa. Wannan shine bayanin da muka samu daga Cif Registara da kansa a wata tattaunawa ta gidan radiyo na tsawon awa daya.
“Amma duk waɗannan kame-kame ne, ba gaskiya ba ne. Akwai batutuwa da yawa masu alaƙa da waɗannan duka. Wani muhimmin al’amari shi ne, ni da Majistare Umar Salihu Kokani da Majistare Halima Umar, duk mun nuna sha’awar a daukaka matsayinmu zuwa alkalan Kotuna Jihar, wanda hakkinmu ne, a duk lokacin da aka fitar da sanarwar gurabun mukamin Alkalin Babbar kotun mu nema saboda matsayinmu ya kai na mu nema,” inji Majistare Mustapha Umar Maccido.
“Kuma ka’idojin NJC a fili take, a cikin ka’idar NJC ta shekarar 2014 na nadin mukamai na ma’aikatan shari’a wanda ya bukaci a rika tallata guraben da ake da su a babban kotun Jihar.
“Haka kuma, wannan ka’ida ta bukaci a aika da tallar zuwa jihohi 36 na tarayya da kuma babban birnin tarayya Abuja domin sanar da duk ‘yan asalin jihar Kebbi da ke kowace jiha masu sha’awar neman mukaman.”
A cewarsa, ta wannan kafar ne hukumar shari’a ta jihar za ta iya fitar da ‘yan takarar da ba su cancanta ba. Ya ci gaba da bayyana cewa akasin haka, ba su bi ka’idojin hukumar NJC da ta ce dole ne su tallata guraben ba.
“Sai dai sun buga wata ‘yar karamar takarda a kusurwa daya a hedikwatar babbar kotun jihar Kebbi, Birnin Kebbi, suka manna wata a kotun daukaka kara ta Shari’a inda babu Lauya.
“Ba su yi wa shugaban kungiyar lauyoyin Nijeriya (NBA) reshin Jihar kwafi ba, ba su mika wa shugaban kungiyar majistare ta kasa (MAN) reshin jihar Kebbi kwafin ba. Don haka, ba su tallata shi ba kamar yadda shawarar NJC ta bayar.
“Don haka da wannan muka yi imanin cewa Babbar jojin Jihar Kebbi ya saba ka’idar NJC wadda ba bisa tsarin ba ne. Ba wai kawai tsarin tallan ya kamata ya kasance na kwanaki 21 ko makonni biyu ba, amma sun lika tallar su a ranar 5 ga Oktoba, kuma sun cire shi a ranar 6 ga Oktoba, kuma wa’adin da aka bayar a cikin tallan ya kasance 7 ga Oktoba, ga masu sha’awar.
“Wato ma’ana, sun ba da kuraren lokaci kwana ne domin su maye gurbin da ke akwai na batare da wasu sun nema. Saboda haka muna ganin cewa tsarin na yaudara kawai, inji Majistare Mustapha Umar Maccido”.
“Duk dakatarwar aka yi muna saboda mun nemi mukaman Babbar Alkalin Babbar kotun Jihar ne. Wannan shi ne kawai dalili. Domin daidaituwa, wannan ba zai iya faruwa kawai ba. Na nema, ya nema kuma ta nema kuma mu kadai ne ke fuskantar wannan dakatarwar da cin zarafi a duk cikin Majistare na Jihar, in ji Mustapha Umar-Maccido”.