Idris Aliyu Daudawa" />

An Danganta Karuwar Cutar Hanta Da Yawan Shan Barasa —Rahoto

Masu bincike sun dora alhakin yawanmace macen da ake yi a Amurka, saboda yawan shan barasa ko kuma giya da ake yi.

Shi dai wannan binciken da aka yi a jami’ar Michigan an gano cewar  da yawan mutuwar da ake samu saboda cirrhosis (matsananciyar cutar Hanta) ko kuma cutar Hanta, ana samun karuwar al’amarin a kasar.

Mujallar  Medical  News Today ce ta wallafa cewar su masu binciken, sun lura da cewa a Amurka ana samun karuwar mutane wadanda suke kamuwa da cutar cirrhosis, saboda yawan shan giya.

Cutar Cirrhosis ana kamuwa da ita ne saboda yawan matsalolin da suka shafi lafiya, da suka hada da hepatitis C, ko kuma cutar Hantar da take da kitse.

Wanda ya shugabanci shi binciken Elliott Trapper wanda shi kwararre ne akan sutar data shafi Hanta, wanda kuma daga Jami’ar Michigan da abokin aikin shi, Neehar Parikh, sun lura da cewar daga shekarar 1996 zuwa 2016, an samu karuwar yawaitar mutuwa , a dalilin cirrhosis daga cikin jihohi 49 na 50 ake dasu a Amurka.

Masu binciken sun gano cewar an samu karuwar mutuwar jama’a da kashi 65 cikin dari, sanadiyar  cutar cirrhosis, bugu da kari kuma giya ita ce  a gaba, a wata cutar da za a kamu da ita gaba, na cututtukan Hanta.

Amma kuma wani abin mamaki shi ne matasa ne abin ya fi shafa, binciken ya gano cewar matasa ,masu shekara 25 zuwa 34, su fafaren fata ne daga kasashen Amurka, Indiya, da kuma Hispanic, sune wadanda suka fi kamuwa da wannan al’amarin.

Ana samun karuwar yawan mace mace a sanadiyar cutar ko wacce shekara, tsakanin matasa da kashi 10 da rabi ko wacce shekara.

Mr Tapper ya bayyana cewar su suna tunanin cewar zasu samu wani ci gaba, idan abin yazo ga yawan mutuwa, saboda cutar Hanta ‘’Amma kuma wannan abinda muka gani ya kawar da dukkan shakku’’

‘’Koda ma bayan hepatitis C har yanzu muna dawasu ayyukan da zamu yi’’.

An dai samu babban ci gaba akan maganin hepatitius C, wannan kuma ana sa ran abin zai samu nasaba da mutuwar da take da alada da cututtukan Hanta.

‘’Muna tsammanin da akwai wata nasaba tsakanin yaaitar shan giya da kuma, rashin aikin yi, ga kuma al’amarin daya shafi  matsalar tattalin arzikin data damu duniya, amma kuma nan bukatar wani abinciken.’’

Lokacin da aka yi shekaru bakwai ana nazarin an samu  mutuwar mutane 460 da kuma 760, a sanadiyar cirrhosis.

Daga ciki ku san daya bisa uku na, suna da nasaba da kansar Hanta wadda ake kira ‘hepatocellular carcinoma’ wannan kum ay faru ne sanadiyar cirrhosis.

Parikh ya bayyana cewar karuar mutuwar da ake samu saboda Hanta, wannan ya nuna da akwai matsala wadda ta shafi kulawa da kuma maganin ita cutar.

Kamar yadda su binciken suka ce jihohin da suke da matsala danagane da mutuwar cirrhosis, an fi samun hakan a Kentucky, Alabama, Arkansas, da kuma New Medico, jiha daya ce kawai ta nuna an samu raguwar kananan matasa a Maryland.

Masu rubuta rahoton sun bayyana cewa, ana iya kaucewa aukuwar cutar hanta sakamakon kwankwadar barasa.

Sun kuma bukaci kasashe su fito da tsare tsaren da zai dakile yawaitar shan barasa, kamar kara haraji da kuma rage tallace tallacen barasa a kafafen sadarwa.

 

Exit mobile version