An fara aikin sabunta Babban Masallacin Juma’a na Sarkin Zazzau Abdulkarim, wanda ke Kofar Fadar Zazzau da kwanaki ya rushe.
Masallacin ya kasance a rufe tun cikin watan Augustan shekarar da ta gatlbata ta 2023, bayan faduwar wani bangare na masallacin wanda yai sanadiyyar rasa rayukan wasu mutum takwas da samun raunikan a cikin Masallacin.
- Harin ‘Yan Bindiga: Jama’a Sun Yi Zanga-zanga A Kaduna, Sun Nemi Taimakon Sarkin Zazzau
- Sarkin Zazzau Ya Nuna Damuwa Kan Satar Shanu Fiye Da 1,000 A Masarautarsa
Idan za a iya tunawa dai wannan bayan rugujewar masallacin, Mai Martaba Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, ya kafa kwakarran kwamitin domin samar sabunta ginin Masallacin.
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma Sardaunan Zazzau, Arch. Muhammadu Namadi Sambo, ne ke jagorantar wannan kwamitin na sabanta ginin Masallacin.