Shugaban kwamitin sabon mafi karancin albashi na Jihar Borno, Dr. Babagana Mallambe, ya sanar da cewa ma’aikatan jihar sun fara karbar sabon albashin Naira 70,000.
Karin albashi, wanda gwamnatin jihar ta amince da shi, an yi shi ne domin inganta rayuwar ma’aikatan jihar.
- Kamfanin Google Ya Bai Wa Nijeriya Tallafin N2.8bn Don Bunkasa Tattalin Arziki
- Yawan ‘Yan Kasuwa Na Kasashen Waje Da Suka Halarci Canton Fair A Wannan Karo Ya Kafa Tarihi
Dr. Mallambe, wanda shi ne kwamishinan tsare-tsare da kasafin kudi, ya bayyana jin dadinsa game da wannan ci gaba a taron manema labarai a Maiduguri.
Dr. Mallambe, ya yaba wa Gwamna Babagana Zulum bisa jajircewarsa wajen inganta walwalar ma’aikatan Borno.
Shugaban ma’aikatan jihar, Barista Fannami, ya karfafa wa ma’aikata gwiwa da su yi aiki tukuru a matsayin hanyar yaba wa gwamnatin jihar kan karin da ta musu.
Sai dai, shugaban kungiyar kwadago, Kwamared Inuwa, ya yi wa gwamnatin jihar godiya, amma ya bukaci a kara wa ma’aikatan kananan hukumomin jihar 27 albashi.