Hukumar kula da tashoshin jiragen kasan Nijeriya (NRC) ta bayyana fara sayar da tikitin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna ta yanar gizo. Shugaban hukumar NRC, Mista Fidet Okhiria shi ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Laraba a garin Abuja. Ya ce, a halin yanzu an bara gwaji ne na tsawan mako kafin a gudanar da shi a ranar 20 ga watan Junairun da muke ciki.
“Muna sanar da fara sayar da tikitin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna a yanar gizo a yau. Mun yi kokarin fara gwaji na tsawan mako guda, inda bayan nan za mu kaddanar da shi a ranar 20 ga watan Junairu a ma’aikatar sufuri ta tarayya.
“Sayar da tikitin ta yanar gizo yana da matukat mahimmanci domin zai sa mutane su sayi tikiti cikin sauki a yanar gizo musamman ma a wannan lokaci na bayar da tazarar saboda cutar Korona,” in ji shi.
A cewar Okhiria, sayar da tikitin ta yanar gizo shi ya fi dacewa domin zai magance manyan matsalolin tsaro da kasar nan take fama da shi. Ya kara da cewa, za a tabbatar da cewa an samar da tikitin a yanar gizo ga dukkan fasinjoji jirgin kasan tare da daukan hotona saboda wasu dalilai na gaggawa.