A Australiya tsuntsayen Jinjimi na daga cikin dabbobin da aka fi kyama a kasar.
Tsuntsun jinjimi ya shahara wajen hanyar da yake bi wajen farauto abincinsa a ko’ina ya same shi, ta hanyar shiga cikin kududdufi da fautar abinci a hannun mutane.
To amma da alama tsuntsun na kokarin sauya mummunar hanyar farautar abincinsa da aka san shi da ita.
Ya fara koyon yadda zai zakulo tare da cin kwadin da al’ummar kasar ke matukar kyama da ki saboda gubar da suke dauke da ita a jikin fatarsu.
Kwadin wadanda suka fara bayyana a kasar a shekarun 1930, babu wata dabba da ke cin namansu, abin da ya sa yawansu ya zarta na sauran dabbobi a kasar.
Fatar kwadin na dauke da wani sinadarin guba, wanda kwazon ke saki da zarar wata dabba ta kai masa farmaki, lamarin da zai yi sanadiyyar mutuwar dabbar nan take sakamakon bugun zuciya.
Emily Bincent ta sha mamaki lokacin da al’ummar kasar suka fara wallafa hotuna da bidiyon tsuntsun yayin da yake wasa da kwadin.
Tsuntsaye masu ban al’ajabi da hikima
Misis Bincent wadda ke gudanar da wasu shirye-shirye game da rayuwar dabobi a gidauniyar Watergum, ta ce wannan lamari ya bai wa mutane da dama mamaki musamman a gabashin kasar.
Ta shaida wa BBC cewa suna matukar mamakin yadda tsuntsayen na Jinjimin ke wasa da kwadin ta hanyar matse ruwan gubar da ke jikinsu.
Baya ga haka su kan binciko kwadin a duk wuraren da suke kamar cikin ruwa tare da zakulo kwadin a can karkashin ruwa”.
Ta ce lallai abin al’ajabi ne yadda tsuntsayen suka koyi yadda za su raba kwadin da gubar da ke jikin fatarsu kafin su cinye su. ”Abin akwai ban al’ajabi”.
Ba wannan ne karon farko da aka ga tsuntsaye na cin kwadin ba, kamar yadda Farfesa Rick Shine ya shaida wa BBC.
Guba ba ta faye yi musu illa ba, kamar sauran dabbobi irinsu macizai da kadoji.
To amma idan gubar ta yi musu yawa suna iya mutuwa, kamar yadda Farfesa Shine ya fada.
Yayin da kwadin suka yadu a fadin kasar Austariya, sauran tsuntsaye irin su shaho da hankaka ka iya koyo tare da sabawa da cin naman kwadin.
Su kan dauki kwadin tare da fyede su domin cin naman kayan cikinsu, su bar sauran gangar jikin ba tare da sun taba shi ba.
Wannan shi ne karon farko da Farfesa Shine – wanda ya kwashe shekara 20 yana nazari a kan kwadi – ya taba jin wani tsuntsu na amfani da wannan hanyar wajen cin naman kwadin.
Hakan ya nuna cewa tsuntsaye ne masu basira da fasaha, in ji misis Bincent.
“Su kan tilasta wa kwadin rabuwa da gubar da ke jikinsu da kansu, ta hanyar matse kwadin har sai ruwan da ke dauke da gubar ya fice daga jikin fatar kwadin.
Rage yawan kwadin
Farfesa Shine da Misis Bincent duka sun ce wannan wata alama ce da ke nuna yadda dabbobin kasar ke kokarin sabawa da kwadin, wadanda a yanzu ake hasashen yawansu a kasar ya zarta biliyan biyu.
Sannu a hankali wasu dabbobin na gane yadda za su mu’amalanci kwadin ‘wadanda ba a farautarsu’.
Wasu na ganin cewa wasu dabbobin na samun sauyi ta fuskar halittarsu lamarin da ke sa raguwar illar guba a jikinsu.
Ga kuma tsuntsaye irinsu su Jinjimi wadanda suka gano hanyar cin kwadin ba tare da wata illa ba.
Hakika hakan zai taimaka wajen kawo raguwar yawan kwadin a fadin kasar.
Haka kuma akwai tsuntsaye irinsu su Jinjimi wadanda suka gano hanyar cin kwadin ba tare da wata illa ba.
Inda hakan zai taimaka wajen kawo raguwar yawan kwadin a fadin kasar.
Farfesa Shine ya ce tsuntsayen Jinjimi na kokari wajen rage yawan wadannan nau’i na kwadi masu cike da hatsarin gaske a kasar.
“Wadannan tsuntsaye na aiki kamar jami’an tsaro na boye wajen rage yawan kwadin a duk shekara”, in ji Farfesa Shine.
Hakika muna godiya ga wadannan tsuntsaye da a baya al’ummar Australiya ke kyamata.