Connect with us

LABARAI

An Girmama Sam Nda-Isaiah Da Sarautar ‘Aare Baaroyin’ Na Akure

Published

on

Shugaban rukunin kanfanin buga jaridar LEADERSHIP, Mista Sam Nda-Isaiah, ya samu sarautar gargajiya ta ‘Aare Baaroyin na masarautar Akure’, Sarkin masarautar Akure, Oba Ogunlade Aladetoyinbo Aladelusi, Deji na masarautar Akure, ya nada masa wannan sarauta. Sarkin ya bayyana shawarar nada Nda-Isaih wannan mukamin ne a bayan da majalisar sarkin ta amince da yin haka a ka kuma sanar da shi ta wasikar da wata tawagar Sarkin ta kawo masa a gidansa dake Abuja jiya.
Tawagar wanda, wani basarake daga masarautar Cif Afolabi Fayehun, Edemo na masarautar Akure, ya jagoranta ta bayyana cewa, Deji na Akure tare da majalisar masarautarsa sun amince da bashi wannan sarautar ne saboda nasarar daya samu a fagen buga jarida a fadin kasar nan.
Cif Fayehun ya kuma kara da cewa, “Bayan nazari mai tsawon lokaci, Deji na Akure da ‘yan majalisarsa sun gano cewa Sam Nda-Isaiah dan Nijeriya ne da baya nuna banbanci a harkokinsa yana kuma hankoron neman ci gaba ga dukkan ‘yan Nijeriya, a kan haka ne mai martaba ya umurci mu yi takakkiyar kawo masa wasikar da kanmu har gida. “
Da yake mayar da martini, mawallafin rukunin jaridar LEADERSHIP, Sam Nda-Isaiah, ya yaba wa Deji na Akure a bisa wannan karrama war da aka yi masa ya kuma yi alkawarin ci gaba da hulda da masauratar don kawo ci gaba.
Nda-Isaiah ya kuma kara da cewa,”na yi matukar mamaki dana samu labarin za a bani wannan sarautar, duk da ban san sa bas hi ma bai sanni ba. wannan wani babban karramawa ne ina kuma mautkar godiya.
“lallai wannan zai dzama wani harshashi na ci gaba da huldar arziki tsakani na da wannan masarauta mai albarka, za muyi huldar da zai amfane mu gaba daya”.
A babban ofishin kamfanin LEADERSHIP, tawagar Sarkin sun bukaci kanfanin jaridar ta taimaka musu wajen tallata tarihin masarautar ga al’ummar duniya gaba daya.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: