• English
  • Business News
Saturday, October 25, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Gudanar Da Bikin Da Ya Shafi Makamashi Na Nan Gaba A Birnin New York

by CGTN Hausa and Sulaiman
1 year ago
New York

A lokacin da ake shirin kaddamar da taron makomar dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya, an gudanar da wani biki mai taken “Makamashi na nan gaba” a birnin New York na kasar Amurka, a ranar 21 ga wata.

Kasashen da suka halarci bikin sun fitar da “Sanarwar makamashi na nan gaba”, da nufin inganta mu’ammala, da hadin gwiwa a fannin makamashi tsakanin mabambantan kasashe, tare da sa kaimi ga sauyawar tsare-tsaren makamashin duniya, da neman samun ci gaba mai dorewa ta fuskar harkar makamashi.

  • PDP Ta Mayar Da Martani Mai Zafi Ga APC Kan Neman Ayyana Dokar Ta-ɓaci A Zamfara
  • Kotu Ta Ba Da Belin Mawaki P Diddy Mai Safarar Mata

Hukumar hadin gwiwar kasashen duniya a fannin makamashi ta yanar gizo ta Internet, wadda kasar Sin ta kaddamar da aikin kafa ta, da kuma ofishin tsara dabaru na neman ci gaba mai dorewa na MDD ne suka karbi bakuncin bikin, inda sama da baki 200 daga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 30 suka halarci bikin.

LABARAI MASU NASABA

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

A wajen bikin, zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Fu Cong, ya bayyana a cikin jawabinsa cewa, yadda za a gina duniya mai tsafta da kyan gani, da tabbatar da makomar dan Adam mai kyau, wani babban batu ne da ke bukatar tunanin daukacin gamayyar kasa da kasa tare. Ya kamata al’ummomin kasa da kasa su karfafa hadin kai, da daukar matakan da suka dace wajen tinkarar kalubaloli, irinsu tsanantar sauyin yanayin duniya, da yawan aukuwar bala’o’i a kai a kai.
Kaza lika a sa kaimi ga daidaita makamashi cikin adalci, da gaggauta aiwatar da manufofin neman ci gaba mai dorewa.

Jami’in na Sin ya yi bayani kan nasarorin da kasar Sin ta samu a fannin raya kasa da kare muhalli, a cikin ‘yan shekarun nan, inda ya yi nuni da cewa, kasar Sin ita ce kasar dake kan gaba wajen sauya tsarin raya tattalin arziki zuwa nau’in kare muhallin halittu, mai sa kaimi ga hadin gwiwar kasa da kasa a fannin daidaita makamashi, kana mai ba da gudummawa ga harkokin kula da makamashi da aikin kyautata yanayin duniya, yayin da kokarin kare muhalli ke zama tushe ga tsarin zamanantarwa na kasar Sin.

A nasa jawabin, manzon musamman na babban magatakardan MDD kan ayyukan daidaita yanayi Selwyn Hart, ya yabawa kasar Sin bisa gagarumar gudummawar da ta bayar a fannin raya tattalin arzikin duniya, tare da tabbatar da ingancin muhallin halittun duniya. Har ila yau, ya jaddada wajibcin mai da hankali kan maganar adalci yayin da ake sauya salon makamashi zuwa mai tsabta a duniya.

A cewarsa, a halin yanzu, yawancin jarin da ake zubawa a bangaren makamashi mai tsabta a kasashe masu sukuni suke, yayin da kasashe masu tasowa da dama suka kasa samun isashen jari. (Bello Wang)

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take
Daga Birnin Sin

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan
Daga Birnin Sin

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 24, 2025
Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa
Daga Birnin Sin

Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

October 24, 2025
Next Post
Tsarin Tantance Ayyukan Likitanci A Sararin Samaniya Zai Ingiza Nasarar Binciken Samaniya

Tsarin Tantance Ayyukan Likitanci A Sararin Samaniya Zai Ingiza Nasarar Binciken Samaniya

LABARAI MASU NASABA

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

Fansho Da Garatuti A Kano: Yau Fari Gobe Tsumma (3)

October 25, 2025
Gwarzon Gwamnan 2025, Biodun Abayomi Oyebanji

Babban Sarki Oweizide Ekpemupolo (Tompolo): Hiddimta Wa Al’umma Ba Tare Da Gajiyawa Ba

October 25, 2025
Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

Kasar Sin Ta Nemi Amurka Ta Dakatar Da Hare-haren Shafin Intanet Kan Muhimman Kayayyakinta Nan Take

October 24, 2025
Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

Ba Zan Kwatanta Matsayina Da Na Sarkin Bauchi Ba – Sabon Sarkin Duguri

October 24, 2025
Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

Gwamnatin Kaduna Ta Gano Ma’adanin Zinari Da Tagulla Da Za Su Haɓaka Tattalin Arziƙin Jihar

October 24, 2025
An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

An Kebe Ranar 25 Ga Oktoba A Matsayin Ranar Tunawa Da Kawo Karshen Mulkin Mallakar Japan A Yankin Taiwan

October 24, 2025

Gwamnatin Katsina Ta Ƙara Samar Da Dakarun Tsaro 200 Domin Maganace Ta’addanci

October 24, 2025
Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

Sin Ta Saka Burikan Da Za Ta Cika A Shekaru 5 Masu Zuwa

October 24, 2025
Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

Jam’iyyar NNPP A Kaduna Ta Ƙaryata Batun Tsige Shugabanta

October 24, 2025
An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan

An Shirya Harba Kumbon Shenzhou-21 A Kwanan Nan

October 24, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.