An Gudanar Da Taron Mata Masu Da’awah Na Jihohin Arewa Karo Na Goma Sha Uku A Kebbi

A jiya ne kungiyar mata masu Da’awah ta kasa a karkashin jagorancin Hajiya Maryam Idris Abubakar sun gudanar da taron mata masu Da’awah na jihohin Arewacin Nijeriya karo na goma sha uku a garin Birnin kebbi a jiya .
Taron dai an gudanar da shine a dakin taro da ke a kwalejin Tarayya watau “ Waziri Umaru federal polytechnic Birnin-kebbi “ da aka fi sani da suna” shehu kangiwa conbocation centre” na kwalejin . Hakazalika akwai mallamai da aka gyato da zasu gabatar da kasidu masu taken “matsalar shaye-shaye a tsakanin matasa da ‘yan mata da kuma muhimmancin mata a cikin Da’awah a kasar Nijeriya da kuma sauran matsaloli da ke addabar tarbiyar yaranmu domin fadakar ga jama’a da kuma jawo hankalisu kan matsalolin da ke addabar ‘ya’yamu a cikin kasar mu Nijeriya, malaman da zasu gabatar da kasidun sun hada da sheikh Bala Lau, sheikh Kabiru Haruna Gombe , sheikh Abubakar Giro Argungu, Ferfesa Mukhatar umar Bunza, ferfesa Isah Maishanu da kuma Dakta Mansur Ibrahim.
Sauran malaman kuwa sun hada da sheikh Mufti Ismail Menk, Sheikh Jabir Mai hula, sheikh Ahmad Ibrahim Suleiman kano a matsayin mai alramma da kuma malam Rabi Isah Abubakar da kuma sauransu .
Haka kuma a yayi gabatar da kasidun sheikh mufti Ismail Menk, ferfesa Isah Maishanu da kuma ferfesa Mukhtar Umar Bunza sun bayyana cewa tarbiyar yaranmu na ga uwaye mata da kuma uwaye maza domin sune Allah ya daurawa hakkin tarbiyantar da yaransu domin duk wanda Allah yaba yaro tau an bashi kiyo ne kuma gobe kiyama sai Allah ya tambaye shi . Har ilayau sun kara da cewa “uwaye mata sun fi zama kusantar ‘ya’ya fiye da uwaye maza domin suna tare dasu koda wane lokaci”, kai musamman sune ke shayar dasu mama , saboda haka akayi kira ga uwaye mata domin kula da tarbiyar yaran .
Bugu da kari sun yi kira kan adalci ga shugabancin yara ko kuma jama’a a wannan kasa ta mu ta Nijeriya , saboda haka sun ja hankalin uwaye da kuma shugabannin jama’a da su jaddada adalci ga jama’ar da suke mulki ko kuma suke karkashinsu.
Daga karkshe sun nemi jama’ar da suka halarci wannan gagarumin taron mata masu Da’awah ta kasa karo na goma sha uku da matar Gwamnan jihar kebbi Dakta Zainab Atiku Bagudu ta dauki nauyin gudanar dashi a jihar kbbi da suyi amfani da ilimin da suka samu a wurin taron domin rage matsalar da ake fama da ita kan lalacewar tarbiyar yaramu a kasar nan .
Da ta ke jawabi a wurin taro mai masaukin baki Dakta Zainab Atiku Bagudu ta yabawa kungiyar mata masu Da’awah a kasar nan kan irin kokarin da suke yi na ganin cewa sun yi Da’awah ga matan musulman kasar nan ga yin ayyukkan da adinin musulunci ke so. Haka kuma t ace” nasan wannan kungiyar ta mata masu Da’awah tun shekaru goma sha daya da suka gabata a birnin tarayya Abuja a lokacin da suke shiga kauyuyukan garin Abuja domin bada tawa gudunmuwarta kan kiwon lafiya a kyauta a matsayata ta likita”, saboda haka na san irin rawar da suke takawa fagen yiwa addinin musulunci aiki.
Hakazalika kungiyar ta mata mai Da’awah ta karrama matar Gwamnan jihar ta kebbi Dakta Zainab Atiku Bagudu da lambar girma a matsayar “Hadimatun Da’awah mata ta kasar nan” a yayi gudanar da taron Da’awar a dakin taro na kwalejin waziri Umaru federal polytechnic da ke a Birnin-kebbi.
Shima mai alfarma sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na ukku, ya bayyana cewa a matsayin sa na shugaban kungiyar musuluncin ta kasa yana tabbatarwa kungiyar mata masu Da’awah ta kasa cewa zasu basu goyun baya da kuma duk wani taimako da zaya karawa kungiyar kwarin gwiwa kan Da’awar da suke yi domin ganin cewa musulunci da musulmai sun ci gaba kuma a samu zaman lafiya a tsakanin ‘yan kasar Nijeriya. Haka ya yi kira ga resu da su kula da tarbiyar ‘ya’yansu domin uwaye mata kune kukafi zaman kusa da yara fiye da uwaye maza , domin kulawarku na da matukar muhimmanci.
Daga karshe godewa gwamnatin jihar kebbi da kuma matar Gwamnan jihar Dakta Zainab Atiku Bagudu wanda yace ‘yarsa ce kan kokarin da tayi na tabbatar da cewa irin wannan taron an gudunar dashi a cibiyar Abdullahi Gwandu , saboda haka Allah yabi ya kuma da aljannar Firdausi.
Haka kuma shima Gwamnan jihar kebbi sanata Abubakar Atiku Bagudu ya gabatar da jawabinsa inda yace” gwamnatin jihar kebbi za tayi hadin gwiwa da kungiyar mata masu Da’awah ta kasa domin fadakar wa a jihar kebbi kan illar rashin sanya yara kananan makarantar boko da kuma illolin rashin yiwa yara sababbin haihuwa alluran rigakafi tun da haihuwar su har zuwa shekaru biyar da haihuwa. Ya kuma godewa matar sa Dakta Zainab kan kokarin tan a ganin cewa ta dauki nauyi gudanar da wannan babban taro na mata masu Da’awa a kasa nan da ake gudunar wa a jihar kebbi wanda ya kasance shine taro na goma sha ukku ga kungiyar .
Ya kuma yi kira ga mahalarta taron musamman iyayen mu mata dasu kara kulawa wurin tarbiyar ‘ya’ya mata da maza musammam ga wannan lokaci da muke ciki na lalacewa tarbiyar yara a cikin al’ummarmu. Daga nan kuma ya godewa dukkan shuwagabannin wannan kungiyar da kuma sarakunan mu na gargajiya da suka amsa gyatar da akayi musu kan wannan taron mata masu Da’awah . saboda haka yana fatar duk wadanda suka halarci wannan da komawa gidajen su lafiya.
Daga karshe itama matar Gwamnan jihar kebbi Dakta Zainab Atiku Bagudu ta bayyana jindadin ta kan karramawar da kungiyar mata masu Da’awah ta kasa sukayi ma da kuma irin fadakarwar da sukayiwa mata da maza a jihar kebbi kan wasu matsaloli da yaranmu ke fuskanta da kuma irin yadda suke sadaukar da kansu wurin Da’awah kan ci gaban addinin musulunci da kuma musulmai. saboda tayi addu’a cewa Allah ya biya su da aljannar Firdausi.
Mahalarta taron sun hada da mai alfarma sarkin musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na uku tare da saraukunan sa wanda kuma shine uban taro, shugaban JIBWIS ta kasa Sheikh Bala Lau tare da wasu makarabansa, Sheikh Kabiru Haruna Gombe, Sheikh Abubakar Giro Argungu, sheikh Mufti Ismail Menk, ferfesa Mukhtar Umar Bunza da kuma sheikh Jabir Mai hula.
Sauran sun hada da ferfesa Isah Mai shanu, Dakta Mansur Ibrahim , Amirar mata mas Da’awah ta kasa Hajiya Maryam Idris Abubakar , matar tsohon mataimakin shugaban kasar
Nijeriya Hajiya Amina Namadi Sambo, matar tsohon Gwamnan jihar Yobe Hajiya Maryam Bukar Abba Ibrahim, matar tsohon Gwamnan jihar Jigawa Hajiya Zara’u Umar Idris da kuma matar mataimakin Gwamnan jihar kebbi Hajiya Halima Sama ila yombe Dabai da matar Gwamnan jihar Zamfara da kuma sauran su, ind wakilai daga jihohi ashirin ne suka halartar taron na mata masu Da’awah ta kasa da aka gudanar a jihar kebbi a jiya.

Exit mobile version