Connect with us

Tauraruwa Mai Wutsiya

An Gurfanar Da Mutum 8 Da Laifin Mallakar Makamai Da Kuma Shiga Kungiyar Asiri

Published

on

An gurfanar da mutum takwas a gaban wata kotun Ogba bisa zargin mallakar makamai da kuma laifin shiga kungiyar asiri. An dai bayyana cewa suna kan yin fada na a kan titi sai wadansu daga cikin mazauna yankin suka kirawo ‘yan sanda ta wayar tarho inda nan take ‘yan sanda suka samu nasarar cafke su. majiyarmu ta labarta mana cewa bayan an bincike su, sai aka samu bindigan hannu guda daya, bindiga kirar AK-47 tare da alburushi guda daya, gatari guda daya sai kuma wukake. Kotu tana tuhumar su da laifuffuka kamar haka, laifin tsorata al’umma, barazana ga zaman lafiya, mallakar makamai ba bisa ka’ida ba da kuma laifin yinkurin fashi da makami.

An dai karanta karan kamar haka “a ranar 12 ga watan Satumba ta shekarar 2018 da misalin karfe 2 na yamma, Olanrewaju Olakunmi, Ibrahim Yusuf, Kuadri Tiamiyu, Taofeek Bello, Adebayo Muiz, James Adeshola, Nurudeen Ewemoje, da kuma Ajakaye Adebowale da sauran mutane suka bayyana a kotun dake kan titin Tinuola cikin Mushin dake Jihar Legas, bisa laifin tsorata al’umma don haka wannan laifi ne wanda ya sabawa sashi na 287 na dokar tsarin mulkin Jahar Legas ta shekarar 2015.”

Bayan haka kuma, “Olanrewaju Olakunmi, Ibrahim Yusuf da kuma Kuadri Tiamiyu a wannan rana kotu ta same ku da karamar bindigan hannu guda daya, adda guda uku, bindiga kiran AK-47 guda daya, karamar gatari guda daya sai kuma wukake, don haka kun aikata laifi kuma za a hukunta ku kamar yadda sashi na 312 1) C) na tsarin dokar Jihar Legas ta shekara 2015 ta tanada.”

Haka kuma, a cikin wannan rana da kuma waje, kotu ta sami “Olanrewaju Olakunmi, Ibrahim Yusuf da kuma Kuadri Tiamiyu da laifin yunkurin yiwa fasinjoji da kuma mazauna yankin Akinbode fashi da makami, don haka za a hukunta ku kamar yadda sashi na 298 3) na kundin tsarin mulkin Jihar Legas ta shekara 2015 ta tanada.”

Lauyan dake kare wadanda ake kara ya musanta laifin da ake tuhumar su da shi.

Alkali mai shari’a Mista O. A. Tanimola ya bayar da belin su a kan kudi naira 100,000 ga kowannan su. Sanna kuma ya dage saurarar karan har sai ranar 22 ga watan Oktoba.

 
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: