Rundunar ‘yansandan Jihar Sakkwato ta ce ta gurfanar da akalla mutane 10 da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne a gaban kuliya.
Kakakin rundunar ‘yansandan jihar, DSP Sanusi Abubakar ne, ya bayyana haka a Sakkwato a ranar Litinin, inda ya ce kama wadanda ake zargin tare da gurfanar da su ya yi daidai da umarnin kwamishinan ‘yansandan Jihar, Mista Muhammad Gumel.
- Da Dumi-Dumi: Kotu Ta Dakatar Da CBN Da Buhari Ƙara Wa’adin Maye Tsoffin Kuɗi
- 2023: Mun Yi Nasarar Gwajin Na’urar Tantance Rajistar Zaɓe – INEC
“Ya umarci hukumomin yankin da su fara kai hare-hare tare da binciken wuraren da aka san suna da ‘yan daba, musamman ofisoshin yakin neman zabe, ofisoshin jam’iyya da gidajen ‘yan siyasa.
“’Yansanda, tare da hadin gwiwar kwamitin tuntuba tsakanin hukumomin tsaro kan harkokin zabe sun kara kaimi wajen dakile manyan laifuka.
“Wadancan wadanda ake zargin sun mallaki muggan makamai, laya da kwayoyi a lokacin da aka kama su,” in ji shi.
Ya kara da cewa kwamishinan ‘yansandan ya gargadi jam’iyyun siyasa da suke ganar da magoya bayansu su daina amfani da makamai a lokacin yakin neman zabe.