An Hako Gawa Da Harshen Zinare Bayan Shekaru 2,000

Zinare

An gano wata gaya mai harshen zinare wanda ta girgiza masu binciken kayan tarihi wadanda suka tono ta tare da wasu gawarwaki 15 a Masar.

Tawagar da aka kafa a tsohuwar gidan Misra, Taposiris Magna ta yi amannar cewa an cire harshen mutumin ne a lokacin da ake binne gawar kuma aka maye gurbinsa da zinariya. Ta ba wa gawar harshen zinare, an yi amannar cewa watakila sun yin hakan ne don neman gafara ga ruhin mai gawar.

Kwarangwal din da aka adana har yanzu yana da kokon kansa, kuma mafi yawan tsarinsa jikinsa yana nan yadda yake, amma abin mamaki shine yadda aka maye gurbin harshensa da na zinariya mai walkiya a cikin bakinsa, wanda nan da nan ya ja hankalin idanun masu binciken kayan tarihi.

An sassaka akwatin gawar ne daga dutse kusan shekaru 2,000, da suka gabata. Masana sun ce, an sassaka akwatunan dutsen ne duba ga yadda mutanen ciki suka yi kama.

Harshen zinariya shine sabon binciken da aka gano daga hakar rami kusan shekaru goma, wanda Jami’ar Santo Domingo ta jagoranta.

A tsawon shekaru goma da suka gabata na aikin hakar, kungiyar ta gano tsabar kudi da yawa a cikin haikalin ‘Taposiris Magna’ wanda ke hade da fuskar Sarauniya ‘Cleopatra BII’, wanda wata kila shekarun kaburburan ya yi daidai da mulkinta.

Exit mobile version