• English
  • Business News
Tuesday, August 26, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Harbe Mutumin da Ya Ƙona Al-Ƙur’ani A Sweden

by Sadiq
7 months ago
in Kasashen Ketare, Manyan Labarai
0
An Harbe Mutumin da Ya Ƙona Al-Ƙur’ani A Sweden
Share on FacebookShare on TwitterShare on WhatsAppTelegram

Wani mutum da ya ƙona Al-ƙur’ani a Sweden ya rasa ransa bayan an harbe shi, a cewar rahotanni daga kafofin yaɗa labarai na ƙasar.

An harbe mutumin mai suna Salwan Momika, mai shekara 38, a daren ranar Laraba a cikin wani gida da ke birnin Södertälje.

  • Wani Ɗan Pakistan Ya Kashe ‘Yarsa Kan Ɗora Bidiyon Kanta A TikTok
  • Isra’ila Ta Dakatar da Sakin Fursunonin Falasɗinawa Duk da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta

A shekarar 2023, Mista Momika ya ƙona Al-ƙur’ani a gaban babban masallacin birnin Stockholm, abin da ya jawo zanga-zanga da bore a wasu ƙasashen Musulmi.

Ƴansanda sun tabbatar da kisansa, inda suka ce sun kama mutane biyar da ake zargi da hannu a lamarin.

Rahotanni sun nuna cewa an harbe Momika ne a lokacin da yake watsa bidiyo kai-tsaye a shafukan sada zumunta.

Labarai Masu Nasaba

Zargin Babban Hadimin Gwamnan Kano Ya Karkatar Da Kuɗaɗen Jama’a Ba Gaskiya Ba Ne

Rashin Tsaro: Ana Ƙoƙarin Ganin Ƙarshen Haƙurin Arewa – ACF

Mista Momika ya yi zanga-zanga da dama da ke nuna ƙin jinin Musulunci, lamarin da ya haddasa bore a ƙasashe da dama.

A lokacin da ya ƙona Al-ƙur’ani, an yi bore a ofishin jakadancin Sweden da ke Bagadaza, inda aka kori jakadan ƙasar daga birnin.

Gwamnatin Sweden ta ce ta ba shi izinin yin zanga-zangar, bisa hujjar cewa yana da ‘yancin faɗar albarkacin baki, kamar yadda dokar ƙasar ta tanada.

Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe

Shiga zaurenmu na WhatsApp

Tags: Alkur'aniKisaSalwan MomikaSweden
ShareTweetSendShare
Previous Post

Isra’ila Ta Dakatar da Sakin Fursunonin Falasɗinawa Duk da Yarjejeniyar Tsagaita Wuta

Next Post

Kafar CMG Ta Samu Nasarar Yayata Shirin Shagalin Murnar Bikin Bazara A Kasashen Waje

Related

Mauludi: Gwamnatin Kano Ta Sake Ɗage Ranar Komawa Makarantu
Manyan Labarai

Zargin Babban Hadimin Gwamnan Kano Ya Karkatar Da Kuɗaɗen Jama’a Ba Gaskiya Ba Ne

10 hours ago
Rashin Tsaro: Ana Ƙoƙarin Ganin Ƙarshen Haƙurin Arewa – ACF
Manyan Labarai

Rashin Tsaro: Ana Ƙoƙarin Ganin Ƙarshen Haƙurin Arewa – ACF

13 hours ago
Gwamnatin Sokoto Ta Ƙaryata Rahoton NBS Kan Talauci, Ta Ƙaddamar Da Sabon Bincike
Manyan Labarai

Gwamnatin Sokoto Ta Ƙaryata Rahoton NBS Kan Talauci, Ta Ƙaddamar Da Sabon Bincike

15 hours ago
Harin Asibitin Gaza Ya Halaka Mutane da Dama, Ciki Har da Ƴan Jarida
Kasashen Ketare

Harin Asibitin Gaza Ya Halaka Mutane da Dama, Ciki Har da Ƴan Jarida

16 hours ago
Ƙungiyoyin Farar Hula Sun Nemi A Dakatar Da Jami’an Gwamnatin Kano
Manyan Labarai

Ƙungiyoyin Farar Hula Sun Nemi A Dakatar Da Jami’an Gwamnatin Kano

21 hours ago
Tinubu Ya Isa Brazil, Zai Nemi Masu Zuba Jarin Biliyoyi A Noma, Makamashi Da Fasaha
Kasashen Ketare

Tinubu Ya Isa Brazil, Zai Nemi Masu Zuba Jarin Biliyoyi A Noma, Makamashi Da Fasaha

22 hours ago
Next Post
Kafar CMG Ta Samu Nasarar Yayata Shirin Shagalin Murnar Bikin Bazara A Kasashen Waje

Kafar CMG Ta Samu Nasarar Yayata Shirin Shagalin Murnar Bikin Bazara A Kasashen Waje

LABARAI MASU NASABA

An Yi Bikin Mu’ammalar Al’Adu Na SCO Na 2025 A Beijing

An Yi Bikin Mu’ammalar Al’Adu Na SCO Na 2025 A Beijing

August 25, 2025
Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Sin Ta Yi Rawar Gani A Fannin Bunkasa SCO

Kuri’ar Jin Ra’ayin Jama’a Ta CGTN: Sin Ta Yi Rawar Gani A Fannin Bunkasa SCO

August 25, 2025
CGTN Poll: Ba Da Kariya Shi Ne Tuna Baya—-Shekaru 80 Bayan Yakin Duniya Na II

CGTN Poll: Ba Da Kariya Shi Ne Tuna Baya—-Shekaru 80 Bayan Yakin Duniya Na II

August 25, 2025
Gwamnatin Tarayya Ta Yi Hasashen Ambaliyar Ruwa A Jihohin Arewa 15

Gwamnatin Tarayya Ta Sake Gargadin Jihohin Arewa 9 Kan Afkuwar Ambaliya 

August 25, 2025
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga 3 Da Kubutar Da Mutum 16 Da Aka Sace A Kaduna

ECOWAS Za Ta Kaddamar Da Rundunar Yaki Da Ta’addanci Mai Jami’ai 260,000

August 25, 2025
Za A Watsa Shirin “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” a Manyan Kafofin Watsa Labarai Na Kasashen SCO

Za A Watsa Shirin “Sha’awar Xi Jinping Ga Al’adu” a Manyan Kafofin Watsa Labarai Na Kasashen SCO

August 25, 2025
Mauludi: Gwamnatin Kano Ta Sake Ɗage Ranar Komawa Makarantu

Zargin Babban Hadimin Gwamnan Kano Ya Karkatar Da Kuɗaɗen Jama’a Ba Gaskiya Ba Ne

August 25, 2025
Wani Rahoton Kasar Sin Ya Kalubalanci Halaccin Ayyukan Amurka Bisa Dogaro Da “’Yancin Zirga-zirga”

Wani Rahoton Kasar Sin Ya Kalubalanci Halaccin Ayyukan Amurka Bisa Dogaro Da “’Yancin Zirga-zirga”

August 25, 2025
Burkina Faso Da Mali Sun Yi Watsi Da Taron Sojojin Afirka A Nijeriya

Burkina Faso Da Mali Sun Yi Watsi Da Taron Sojojin Afirka A Nijeriya

August 25, 2025
Beijing Zai Bunkasa Amfani Da Fasahohin Zamani A Wuraren Adana Kayan Tarihi

Beijing Zai Bunkasa Amfani Da Fasahohin Zamani A Wuraren Adana Kayan Tarihi

August 25, 2025
Talla

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In

Add New Playlist

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.