An shirya taron bita na kwana daya kan yadda fulani makiyaya za su rika shuka ciyawa a Jihar Kaduna, domin ciyar da shanu da sauran dabbobinsu tare kuma da bunkasa kasuwancinta (ciyawar), tuni dai aka ware musu kadadar da za su fara shuka wannan ciyawa.
Haka zalika, matan fulani makiyayan kuma za a ba su shanu domin su fara samar da wadatacciyar madara a fadin jihar da kuma kasa baki-daya.
- Majalisa Za Ta Yi Bincike Kan Hakar Ma’adanai Da Kalubalen Tsaro A Arewa
- Sabon Salon ‘Yan Bindiga Na Sace Daliban Jami’a Mata…
Bugu da kari, an yi hakan ne domin samar musu da aikin yi da kuma rage rikicin da ke afkuwa a tsakanin makiyayan da monoma tare kuma da nufin mayar da ‘ya’yan fulani makarantar boko, su samu ilimin zamani.
Kungiyoyin fulani makiyaya biyu masu samar da madara wadanda suka fito daga Kananan Hukumomin Kubau da Chikun da ke Jihar Kaduna ne suka amfana da wannan shiri.
Har ila yau, shirin na daya daga cikin kokarin da take yi na bunkasa tattalin arzikin fulani makiyaya. Cibiyar bunkasa samar da madarar shanu (MBCF), karkashin shirin bunkasa sama wa matasa aikin yi ta hanyar noma da kiwo, wadda kungiyar ECOWAS ta dauki nauyi da wayar da kai.
Da take yin nata jawabin a wajen taron, Jami’ar Shirin Dakta Bilkisu Yusuf ta ce, an samar wannan da shiri ne domin rage yawan matasa marasa aikin yi a tsakanin fulani makiyaya da kuma tallafawa matansu.
Ta kara da cewa, shirin zai bai wa matasa makiyaya dama a kan yadda za su noma ciyawar shanu, a yayin kuma da za a bai wa matan makiyayan shanu; domin samar da wadatacciyar madara.
Bilkisu ta karfafawa matan guiwa kan su bai wa shirin goyon baya, musamman ganin yadda aka samar da shi domin tallafa wa rayuwarsu.
A karshe, wadanda suka amfana da wannan bita, sun yaba wa cibiyar bisa namijin kokarin da take yi na inganta rayuwa tare da alkawarin bayar da goyon baya, domin samun nasarar shirin a koda-yaushe.