Kwamitin albarkatun Gas na fadar shugaban kasa ya kaddamar da cibiyar dake ababen hawa daga amfani da man fetur zuwa amfani da iskar gas a jihar Kaduna (CNG) a wani mataki na gwamnatin tarayya na rage wa jama’a wahalhalun da ake ciki sakamakon janye tallafin mai.
Da yake kaddamar da cibiyar a karshen mako, shugaban kwamitin CNG na fadar shugaban kasar, Zacch Adedeji, ya ce, cibiyar dake motocin ta CNG, an tsara ne domin canza tsarin amfani da man fetur zuwa amfani da iskar gas a motoci.
- Gwamnatin Tarayya Ta Karfafa Shirin Samar Da Motoci Masu Amfani Da Iskar Gas
- An Fitar Da Rahoton Yadda Kamfanonin Sin Ke Sauke Nauyin Al’umma A Afrika
Adedeji ya kara da cewa, cibiyar wata alama ce ta kawo gagarumin sauyi da sauki ga bangaren makamaci.
Ya ce, (Wannan gagarumin sauyi ba kawai ma zai rage kudin kashe ga masu mallakin motoci ba ne, zai kuma taimaka sosai wajen rage iskar carbon.
“A yau, mun cimma wani nasara, samar da tsari mafi inganci da sauki da jama’a za su iya amfani da shi. Dukka wannan na cikin manufar gwamnatin shugaban kasa Bola Tinubu na farfado da kyakkyawar fata a bangaren bunkasa harkokin kere-kere da kiyaye muhalli.
“Cibiyar dake motoci daga mai zuwa gas na cikin yunkurinmu na kawo mafiya ga bangaren makamaci da zai taimaka wa cigaba mai zuwa. Muna sane da cewa samar da sauki ga jama’a na daga cikin muhimmin abun bukata. Kuma CNG shi ne mafitar. Zai rage wa jama’a kashe kudade kamar yadda aka saba na sayen mai domin amfani yau da gobe.”
Shi ma da yake nasa jawabin, daraktan shirye-shirye na P-CNGi, Michael Oluwagbemi, ya ce, shirin CNG, na da kariya sosai kuma akwai saukin da ‘yan Nijeriya za su iya amfani da shi, kana zai bayar da dama wajen tsaftace muhalli, rage kashe kudade da kuma kula da lafiyar muhalli hadi da janyo mafita ga bangaren makamashi.
“Yana da kyau mu tuna cewa wannan cibiyar ba kawai ga Kaduna ba ce; ana maganar kasa ne baki daya da kuma duniya da ke bukatar kawo sauyi wajen kiyaye tsaftar muhalli da samar da sauki a bangaren makamashi.
“A yau mun tsaya kan tubalin kafa tarihi a jihar Kaduna, tare da manufar samar da makamashi mai daurewa cikin sauki, kuma da jama’a za su iya runguma cikin sauki da inganci.
“Wannan kaddamarwar ba kawai bikin bude cibiyar musaya ta CNG ba ce, a’a wani asasi ne na ganin an kawo gagarumin cigaba da zai bayar da dama a kaddamar da irin wannan cibiyar a jihohin Legas da Abuja,” ya shaida.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp