ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Sunday, December 21, 2025
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

An Kaddamar Da Shirin Baje Kolin Inganta Harkar Noma Da Sana’o’i A Kano

by Abdullahi Muh'd Sheka
2 years ago
Noma

LABARAI MASU NASABA

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

ADVERTISEMENT

An bayyana shirin Gwamnati Na Kano CARRES da cewa shi ne shirin da yafi sauran shirye shiryen da ake bijiro dasu da sunan tallafin saukakawa jama’a radadin matsin rayuwa da jama’a ke fama da ita tun bayan faruwar Annobar Korona wadda tayi sanadin durkushewar tatalin jama’a.

Shugaban Hukumar Kano CARES na Jihar Kano Alhaji Rufa’I ne yabayyana haka alokacin da yake zagawa da babban sakataren ma’aikatar gona na Jihar Kano Alhaji Salisu Tahir alokacin shirin da ake na kaddamar da tallafin kayan Noma ga daruruwan matasa maza da mata a Jihar Kano.

  • Tinubu Ya Kori Shugaban Hukumar NASENI Bayan Wata 3 Da Nadinsa
  • Rage Radadin Cire Tallafi: Gwamnati Ta Baiwa  Kowacce Jiha Naira Biliyan Biyu A Kashin Farko

Alhaji Rufa’I ya shaidawa Babban sakataren Ma’aikatar gonan na jIhar Kano cewar wannan hukuma ta himmatu kamar yadda aka bata cikin kudin tsare tsaren wannan hukuma na samar da tallafi kamar bayar da injunan nika, injin malkade, injin ban ruwa mai amfani da hasken rana, kiwon Kaji, samar da hanyoyi a karkara da kuma gina wuraren kewayawa a kasuwanni da wuraren taruwar al’umma.

Hakazalika shugaban hukumar ta Kano CARES  ya bayyanawa mahalarta taron irin yadda majalisar mahaddata alkur’ani suma suka shigo cikin tsarin, musamman ganin suna da kyakkyawan shirin rage kwararar almajirai daga kauyuka zuwa manyan birane tare da kokarin magance matsalar barace barace wadda a halin ke neman zama wata barazana a jihar Kano, don haka sai ya tabbatar da cewa yanzu haka shirye shirye sunyi nisa na sake samar da wani rukunin al’umma da suma ake fatan zasu rabauta da wannan tallafi da Gwamnatin Kano ke saukewa al’ummarta.

Da yake jawabi alokacin da yake ganewa idonsa irin kayayyakin da hukumar ta samar domin rabawa al’umma musamman abinda ya shafi noma, kiwo da sana’o’in dogaro da kai, Dakta Farouk Kurawa ya bayyana farin cikinsa tare da jinjinawa kokarin wannan hukuma wadda yace babu shakka ya fahimci yadda jama’a ke alfahari da ayyukan wannan hukuma ke nuni da kyakkyawan alhairan da ke kunshe cikin manufofi da aikace aikacen hukumar ta Kano CARES.

Shima da yake duba kayayyakin da hukumar Kano CARES ta tanada domin ci gaba da rabawa jama’a, babban sakataren ma’aikatar gona na Jihar Kano Alhaji Salisu Tahir ya nuna gamsuwa da irin kalaman da yaji daga bakin wadanda suka amfana da alhairan wannan hukuma ta Kano CARES, musamman kan batan smaar da hanyoyi a karkara, inda wasu da suka amfana daga Kananan Hukumomi Gazawa da Kura suka bayyana farin cikin al’umarsu bis aaikin hanya da wannan hukuma ta shimfada masu a yankunansu.

Alhaji Salisu Tahir ya jinjinawa kokarin shugabannin hukuma tare da rokonsu da su kara himma wajen sauke nauyin da aka dora masu, sannan kuma ya bukaci wadanda suka amfana da wadanann tallafi iri daban daban da suyi kyakkyawan amfani dashi, domin ganin nan gaba kadan suma sun zama suna cikin wadanda da za su taimaka wa sauran al’umma. A karshe ya yi addu’ar Allah ya sawa damunar mu albarka.

ShareTweetSendShare

MASU ALAKA

Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa
Labarai

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli
Labarai

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta
Kotu Da Ɗansanda

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Next Post
Gwamnan Kaduna

Gwamnan Kaduna Ya Bude Masaukin Dalibai Mai Gado 400 Da Ofishin Hukumar Raya Birnin Zariya

LABARAI MASU NASABA

Zaben Fidda Gwani A APC: Sanatocin Jigawa Sun Rasa Tikitin Komawa Majalisa

APC Za Ta Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa A Watan Maris

December 21, 2025
Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

Mun Shirya Tsaf Domin Lashe Gasar AFCON Ta Bana – Bassey

December 21, 2025
Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

Sarakuna Na Da Rawar Takawa Wajen Kare Muhalli A Nijeriya – Ministan Muhalli

December 21, 2025
Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

Me Ya Sa Ake Fifita Ilimin Boko A Kan Na Addini?

December 21, 2025
Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

Yadda Itacen Dorawa Ke Warkar Da Cututtuka Daban-daban

December 21, 2025
‘Yansanda Sun Kama Ɗan Bindiga Da Kuɗin Fansa Naira Miliyan 5 A Delta

An Cafke Wani Mutum Da Ya Lakada Wa Dansa Duka Har Lahira A Edo

December 21, 2025
Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

Bambance-bambancenmu Shine Ƙarfinmu — Uba Sani

December 21, 2025
Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

Kotu Ta Fara Sauraren Korafe-korafen Dalibai A Kan Jami’ar MAAUN

December 21, 2025
Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Tinubu Ya Sauya Sunan Jami’ar Azare Don Karrama Sheikh Dahiru Usman Bauchi

December 20, 2025
Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

Wajibi Ne Tawagar MONUSCO Ta Wanzar Da Cin Gashin Kai In Ji Wakilin Kasar Sin

December 20, 2025

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.