Rundunar ‘yansandan Jihar Anambra ta yi nasarar cafke wasu ma’aurata da ke da hannu wajen safarar wani jariri dan wata daya.
Rahotanni sun bayyana cewa ma’auratan sun sayi jaririn ne a hannun mahaifiyarsa da ke unguwar Ajah a jihar Legas kan kudi kadan kan kudi naira 30,000.
- An Ceto Mutumin Da Ya Shafe Wata 6 A Hannun ‘Yan Bindiga A Kaduna
- NLC Ta Ki Amincewa Da Umarnin Hana Ma’aikata Saka Dogayen Kaya A Neja
Har yanzu dai ba a bayyana sunayen ma’auratan ba, amma jami’an ‘yansanda sun cafke su a Onitsha lokacin da suke kokarin shiga wata mota da jaririn a ranar Lahadi.
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, kakakin rundunar ‘yansandan Anambra, DSP Ikenga Tochukwu, ya bayyana cewa ‘yansandan sun yi gaggawar ceto jaririn tare da mika shi ga ma’aikatar harkokin mata da kananan yara ta jihar.
Tochukwu ya ci gaba da cewa, an mika ma’auratan ga hukumar hana fataucin mutane ta kasa (NAPTIP) ta jihar domin ci gaba da bincike.
A cewarsa an gano su a lokacin da wani fasinja da ke cikin motar ya sanar da ‘yansanda yana zargin cewa ma’auratan na dauke da jaririn da ba nasu ba.
Ya bayyana cewa mai ba da labarin ya sanar da ‘yansanda cewa ya lura cewa a lokacin da suke tafiya daga Legas, jaririn na kuka, amma matar ta gaza ba shi nono.
Kwamishinan ‘yansandan jihar, CP Aderemi Adeoye, ya yaba wa mutumin kan taimaka wajen ceto yaron.
Ya kuma yaba da kwazo da taka-tsan-tsan da jami’an ‘yansanda suka yi wajen magance lamarin cikin gaggawa.