An Kama Soja Da Akwatunan Albarusai A Tashar Maiduguri 

Daga Muhammad Maitela,

An yi nasarar damke wani sojan Nijeriya mai suna Sanni Mohammed, dauke da akwatunan albarusai biyu wadanda suka kai kimanin 2,000, masu nauyin 7.62mm, kamar yadda ganau suka shaida wa wakilinmu a jihar.

Wannan soja, mai mukamin ‘Lance Corporal’, wanda jami’an kunkiyar motocin sufuri ta NURTW suka kama shi a tashar motocin bas-bas ta Borno Edpress da ke Maiduguri a ranar Litinin, an damke shi ne yana kokarin ficewa da su zuwa Abuja, inda daga bisani suka mika shi ga ‘yan sanda.

Wani bincike ya gano cewa sojan ya na aiki da Bataliyar sojojin musamman ta 198 (Special Forces Battalion), wanad bayanai suka nuna ya nemi hutu daga wajen da yake aiki a garin Damasak a jihar Borno.

Da yake amsa tambayoyin yan-sanda wanda ake zargin ya bayyana cewa ya samu wadannan albarusan ne a wata motar su da ta samu tangarda a sansanin da yake aiki.

karin wasu kayan da aka samu a hannun shi, sun hada da shaidar amincewar tafiya hutun kwanaki uku tare da takardar shaidar gwaji daga asibiti. Har wala yau, kafin hakan rundunar sojoji ta sanar da yan-sanda ba ta bai wa soja wata shaidar asibiti balle ta bulaguro.

Bugu da kari kuma, wata majiyar sojoji ta tsegunta cewa rundunar sojoji ta na zaman jiran dakon yan-sanda su mika mata don gudanar da bincike kan matsalar.

A hannu guda kuma, Kakakin rundunar yan-sandan jihar Borno, Edet Okon, ya ki ya tofa albarkacin bakin shi dangane da wannan batu ba, saboda yadda ya ki cewa uffan kan sakon kar ta kwana da aka tura masa.

Exit mobile version