An kama sojoji biyu bisa alaka da rushewar wani kamfanin hada magungunan bogi a Kasuwar Alaba International, Ojo, Jihar Legas.
A baya, PUNCH Metro ta ruwaito cewa Kwamishinan ‘Yansanda, Olohundare Jimoh, ya sanar da gano tare da rufe wurin sarrafa magungunan a yankin Ojo na jihar.
- An Bukaci Amurka Da Ta Kauracewa Sanya Wasu Sassa Na Muzgunawa Kasar Sin Cikin Kudurin Dokar Tsaron Kasa
- Yawan Jarin Waje Da Kasar Sin Ta Yi Amfani Da Shi A Watan Nuwamban Bana Ya Karu Da Kaso 26.1%
Da yake magana da ‘yan jarida a ranar Laraba a ginin da aka kai samame a titin Alhaji Oki, Mosafejo, Ojo, shugaban ‘yansandan ya bayyana aikin a matsayin babban ci gaba wajen kare lafiyar jama’a.
Harantaccen wurin ana hada magungunan bogi da aka shirya domin sayarwa da kuma amfani da su ga jama’a.
Wata majiya daga rundunar ‘yansanda, wadda ta nemi a sakaya sunanta saboda ba ta da izinin magana kan lamarin, ta shaida wa wakilinmu a ranar Lahadi cewa ana amfani da sojojin wajen rarraba magungunan bogin zuwa sassa daban-daban na Jihar Legas.
Majiyar ta kara da cewa wani tawagar ‘yan sanda daga Ofishin ‘Yansanda na Ojo, karkashin jagorancin Dibisional Police Officer, CSP Olaifa Omolola, ta tare motar yayin da take dauke da magungunan tana kan hanyarta zuwa inda za a kai su.
“Wata tawagar ‘yansanda daga Ofishin ‘Yansanda na Ojo, karkashin jagorancin DPO, CSP Olaifa Omolola, sun tare wata mota dauke da magunguna a cikin motar haya a wani lokaci a watan Satumban 2025, kusa da tashar mota ta St Patrick a Kasuwar Alaba International.
“Daga bisani DPO ta tura jami’an bincike zuwa yankin, inda aka kama wasu mutane biyu sanye da kayan sojoji tare da magungunan da wa’adin amfaninsu suka kare,” in ji majiyar.
A cewar majiyar ‘yansandan, aikin ya kasance mai matukar wahala, domin da farko sojojin sun ki bayyana inda magungunan suka fito da kuma inda ake shirin kai su.
“DPO da kanta ce ta jagoranci binciken. Ta hanyar jajircewarta ne aka gano inda ake hada magungunan.
“Yayin binciken, an gano cewa mutumin da ya fara wannan kasuwanci tun asali ya mutu, amma matarsa da ma’aikatansa sun ci gaba da wannan haramtacciyar harkar,” in ji majiyar.
Haka kuma an gano cewa CSP Olaifa ta ki amincewa da tayin cin hanci mai yawa daga wasu mutane da ba a san ko su waye ba, wadanda ake zargin su ne ke da hannu a harkar magungunan bogi, inda suke yawan kiran ta a waya.
“DPO ta fara samun kiran waya masu ban mamaki daga wurare daban-daban, inda ake tayin belin wadanda ake zargi tare da rokon ta ta fadi duk farashin da take so domin a rufe lamarin, amma ta yi watsi da tayin tare da yin abin da ya dace ta hanyar mika shari’ar inda ya dace,” in ji majiyar.
An kuma gano cewa mutane biyar ne ke da hannu wajen hada magungunan bogi da kuma canza ranakun karewar wa’adin amfani da su, kuma sun fi gudanar da ayyukansu ne cikin dare.
Magungunan bogin da aka kwato daga hannun kungiyar sun hada da ampicillin, promethazine hydrochloride, kuinine hydrochloride, da kuma nau’o’in magungunan zazzabin cizon sauro da sirinji daban-daban.
Wakilinmu ya kuma gano cewa ‘yansanda sun bi diddigin wasu daga cikin magungunan da wa’adinsu ya kare zuwa manyan shagunan magunguna a Festac Town, Satellite Town da kuma Lagos Island.
Ba a samu jin ta bakin kakakin rundunar ‘yansandan jihar Abimbola Adebisi, ba saboda ba ta amsa kiran wayoyinta ba.
Sakon kar-ta-kwana (SMS) da aka aike mata ma ba ta amsa ba har zuwa lokacin da aka kammala wannan rahoto.”














