Mai Bai wa Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaron Kasa (NSA), Nuhu Ribadu, ya ce an kama wasu da ake zargi da hannu a harin da aka kai wa shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya, Joe Ajero.
Ofishin na NSA, wanda ya nuna damuwasa kan faruwar lamarin inda ya ce tun daga lokacin abin ya faru aka fara bincike akai.
- Man Da Nijeriya Ke Hakowa Ya Karu Zuwa Ganga Miliyan 1.35
- Haaland Ya Samu Rauni Yayin Buga Wasan Sada Zumunta
Ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da jamiin yada labarai na mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Zakari Mijinyawa ya fitar.
A wani bangare, sanarwar ta ce, Mai bai wa shugaban kasa shawarar ya bukaci kungiyar kwadago ta janye yajin aikin, domin ya yi Allah-wadai da harin da aka kai wa shugaban na NLC, ya ce an fara kama wddanda ake zargi da kai harin gami da ci gaba da bincike.
Ofishin Mai Ba Shugaban Kasa Shawara Kan Harkokin Tsaro ya damu da ayyana yajin aikin da shugabannin kungiyoyin kwadagon karkashin jagorancin NLC da TUC suka yi a fadin kasar. Ofishin na NSA ya damu musamman game da illolin yajin aikin ga rayuwar talakawan Nijeriya da kuma illar da ke iya haifarwa ga tsaron tattalin arziki da sauran manyan muradun kasa.
Kamar yadda shugabannin NLC suka shaida, nan take ofishin na NSA ya shiga tsakani domin samun labarin halin da shugaban kungiyar kwadago ta Nijeriya Joseph Ajaero ya tsinci kansa a Garin Owerri na Jihar Imo. NSA ya yi bakin cikin faruwar lamarin tare da yin Allah-wadai da lamarin baki daya domin ya saba wa doka da kaidojin yancin fadin albarkacin baki da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatinsa suka yi. Gwamnatin Tarayya ba za ta taba lamuntar irin wannan mummunan aiki ba.
NSA ya bayar da tabbacin cewa za a bayyana sakamakon binciken, inda ya yi kira ga kungiyoyin da su janye yajin aikin.
Kamar yadda lamarin ya faru, an umurci hukumomin da suka dace da su gudanar da cikakken bincike kan lamarin tare da gurfanar da wadanda suka aikata laifin gaban kotu. Ci gaban da ake samu na nuni da cewa an riga an kama wasu da suke hannu a lamarin. Za mu fito da sahihan bayanai game da sakamakon binciken da zarar an kammala shi.
Sanarwar ta kara da cewa, Gwamnatin tarayya ta ofishin NSA, tana kira ga shugabannin kwadago da su janye yajin aikin da suke yi a halin yanzu, su bari a ci gaba da tattaunawa har a cimma matsaya, in ji sanarwar.