Rundunar ‘yansandan jihar Nasarawa ta kama wasu ‘yan bangar siyasa su ashirin da hudu.
‘Yansandan sun ce, sun kama wadanda ake zargin ne a Minki da ke kan hanyar Keffi zuwa Akwanga.
A wata takarda da ya raba wa manema labarai, jani’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar, Muyiwa Adejobi ya ce, wanda aka kaman yaran wani dantakara ne na shekara 2023.
Adejobi ya ci gaba da cewa, wadanda aka kaman su ne suka tayar da zaune tsaye a zabe firamare na mazabar Nasarawa ta yamma.
Jami;an ‘yansandan sun kame wadanda ake zargin ne a wani otal bayan sun gama cin karensu ba babbaka.
Ya ce, daga cikin abubuwan da aka kama a hannun ‘yan sara-sukan akwai bindigogi guda takwasa da kuma wasu bindigogin na gargajiya guda biyu da kwanson harsasai guda talatin da bakwai da kuma riga guda hudu wadda harsashi ba ya iya huda ta.
Sauran abin da aka samu a hannunsu su ne watoti guda ashirin da bakwai sa wukake da kuma guru da layu. Kamar yadda rahotanni suka tabbatar, su dai wadannan ‘yan sara-suka, wasu daga cikin ‘yansiyasa ke amfani da su wajen yin barazana ga abokan adawa, wani loaci har ta kan kai yin fada da zybar da hini.
Adejobi ya ce, yanzu haka ‘yansandan na ci gaba da bincikar wadanda ke hannunsu, wanda kuma ya ce, da zarar sun kammala bincike za su tura wadanda ake zargin zuwa kotu domin yi musu hukunci.sa