Rundunar ‘yansandan Babban Birnin Tarayya, Abuja ta sanar da cafke ‘yan Shi’a akalla 97 wadanda ake zargi da hannu wajen kisan wasu jami’an ‘yansada biyu, bayan wani rikici ya barke a kasuwar Wuse.
Wannan na zuwa ne biiyo bayan umarnin da Sufeta-Janar na ‘Yansanda, ya bayar na kamo ‘yan shi’ar da ake zargi da kashe jami’an ‘yansandan guda biyu.
- Gwamnan Nasir Ya Kaddamar Da Rabon Tallafin Naira Biliyan 6.5 Ga Mutane 65,000 A Kebbi
- Shugaban Gasar Olympics Ta Paris 2024 Ya Aika Da Wasikar Godiya Ga Shugaban CMG
A ranar Lahadi ne, aka yi wata arangama tsakanin ‘yansanda da ‘yan shi’a yayin tattakinsu a Abuja.
‘Yansanda sun ce ‘yan shi’a ne suka farmaki jami’ansu ba tare da wani dalili ba, inda suka hallaka guda biyu.
Wasu daga cikin jami’an da dama kuma suka samu munanan raunuka.
Kakakin rundunar a Abuja, SP Josephine Ade, ta shaida wa Leadership cewa ‘yan shi’a sun yi amfani da duwatsu, adduna da sauran makamai wajen farmakar jami’ansu a yankin Wuse.
Ta ce yanzu rundunar na gudanar da bincike kan wadanda ta kama kafin mika su kotu domin yanke musu hukunci.