Masana ayyukan gona da ke cibiyar binciken dabarun noma, wato Institu For Agricultural Research, wadda ke Jami’ar Ahmadu Bello, sun kammala binciken sabon irin masara da ake kira ‘Tela Maize’ kashi na biyu da suka yi a gonakin gwaji da cibiyar ta mallaka a Zariya.
Farfesa Rabi’u Adamu, shugaban sashin binciken sabbin dabarun noma na wannan cibiya, har’ila yau jagorar binciken samar da sabon irin masarar ya bayyana hakan ga wakilinmu da ke Zariya, jim kadan bayan kammala duba gonar da masanan suka yi gwajin sabon irin na ‘Tela Maize’, bisa sa idon hukumar tantance sha’anin noma da cibiyarta ke Babban Birnin Tarayya Abuja.
Farfesa Rabi’u ya kuma yi bayanin yadda bayan an gudanar da binciken sakamakon da aka samu na masarar da aka shuka, sai kuma aka kona daukacin masarar da aka samu a karshen binciken, ya ce yin haka, umurni ne da hukumar bin ka’ida kan binciken ayyukan noma, da duk abin da ake bincike a kansa, ba zai je ga manoma ba, sai wannan hukumar da aka ambata ta tabbatar an gudanar da binciken bisa tsare – tsaren da aka tsara, daga nan ne sai a dauki matakin na gaba.
Masanin ayyukan gona Farfesa Adanmu ya ci gaba da cewar, a shekara mai zuwa ta 2021, hukumar za ta ba cibiyar binciken ayyukan gona umurnin zuwa gonakin manoma, domin a shuka wannan iri a gonakin na su, daga na ne kuma, a cewarsa, a shekara ta 2022, saiwannan hukuma ta bayar da umurnin raba wannan iri na ‘Tela Maize’ ga cibiyoyin sayar da iri, domin sayar wa ga manoma da suke sassan Nijeriya.
A tsokacin da Farfesa Rabi’u Adamu ya yi na yadda manoma za su shuka wannan sabon iri a shekara ta 2022, ya ce, duk manomin da ya sami wannan irin masara zai noma ta sau biyu, wato rani da damina, abin bukata kawai, a cewa Farfesa Adamu shi ne manoma su yi amfani da shawarwarin da masana ayyukan gona suka basu, tun daga shuka irin ya zuwa girbi.
A game da banbancin wannan sabon irin masara da sauran masara da manoma suka saba shukawa kuwa, ya ce, wannan sabon irin masara, ya na daure ruwa da kuma mallakar kariya daga wasu tsutsotsi da suke lalata masara da zarar ta fara girma.
Farfesa Adamu ya ci gaba da cewar, yanzu haka, masu gudanar da binciken samar da wannan sabon irin masara na ‘Tela Maize’, suna ci gaba da yin bincike ta shuka wannan irin masara da rani, domin gane masarar yadda za a amfana da ita in an shuka ta da rani da kuma matsalolin da za ta fuskanta. Binciken, a cewarsa, zai nuna matakan da za a dauka da zarar an shuka ta rani, wato in damuna ta dauke.
A karshen zantawar da aka yi da Farfesa Rabi’u Adamu, ya ce suna gudanar da binciken wannan sabon irin masara a jihohin da suka hada da Oyo da Ogun da sai kuma ajihohin arewa, a kwai jihohin Kaduna da Katsina da Zamfara da Jigawa da kuma Kano.