A jiya ne, wani matashi mai shekaru 25 ya rasa ransa, a yankin Ishawo cikin Jihar Legas, a lokacin fada tsakanin sad a wanda ya ci cacar raguna. An dai kawo raguna da yawa a kasuwar Gbagada da ke Jihar Legas, saboda shirin babbar sallah. Matasa sun shiga cikin cacan raguna, inda su ke hada raguda guda biyu fada, daga karshe duk wanda ya yi nasara, to shi zai tafi da kudaden da a ka hada zuwa gida.
Majiyarmu ta labarta mana cewa, a cacan da ya gudana a jiya, an samu rikici tsakanin bangarorin guda biyu. Wannan ne ya yi sanadiyyar mutuwar marigayi Yusuf Isiyaka, ta hannun wani matashi mai suna Segun Banji. Sun fara fada inda a ka caka wa marigayen wuka a bangaren kirjinsa na hagu, wanda ya yi sanadiyar mutuwarsa har lahira.
Wani wanda lamarin ya faru a gaban idanunsa mai suna Biola Idowu, ya bayyana cewa, “nan take Banji ya dukufar da gwawowinsa kasa lokacin da ya tabbatar cewa, abokin fadar sa ya mutu. Watakila idan da an garzaya da Isiyaka zuwa asibiti da zai rayu. “Mahukuntar yankin Oke Oko sun samar wa ‘yan sandar yankin Owutu
a wannan lokaci, inda su ka iso wurin da lamarin ya faru cikin gaggawa, wanda ya kai ga cafke wanda a ke zargin. Shi dai wanda a ke zargin ya na zaune ne a gida mai lamba 15 da ke kan titin Araromi cikin yankin Oke Oko. “Sun tafi da wanda a ke zargin a motarsu na sintiri. Sai dai sojojin da ke gudanar da aiki a yankin sun tsayar da ‘yan sandar, inda su ka nemi a ba su wanda a ke zargi, domin ya tsaya a hannunsu har sai sun karo karin ‘yan sanda kafin su tafi da shi. Wasu fusatattun abokanan mamacin su ka farmaki sojojin, inda su ka zargi sojojin da son su kele wanda a ke zargi ya sulale. Daga karshe an mika wanda a ke zargin ga ‘yan sanda lokacin da su ka kara yawa.”
Rundunar ‘yan sanda na yankin Owutu sun tabbatar da wannan kamen, inda su ka bayyana cewa, za a mika wanda a ke zargi ga sashen rundunar ‘yan sanda da ke binciken manyan laifuka da ke yankin Yaba, domin gudanar da cikakken bincike a kan lamarin.