Juventus ta rasa maki 10 bayan wani sabon bincike da aka gudanar kan cinikayyar ‘yan wasa da kungiyar ta yi a baya.
Da farko Juventus ta fuskanci hukuncin da ya sa aka kwashe mata maki 15 a watan Janairu, amma Babbar Kotun Wasanni ta Italiya ta soke hukuncin a watan Afrilu tare da ba da umarnin sake duba lamarin.
- Buhari Zai Kaddamar Da Ayyuka 7 A Ranar Talata –Fadar Shugaban Kasa
- NAHCON Ta Nemi Alhazai Su Biya Kashi 40 Na Dala 250 Na Jigilarsu
A watan Janairun 2023 aka hukunta Juventus, bayan da aka sami kungiyar da laifin bayar da bayanan karya na hada-hadar kudadenta.
An sanar da sabon hukuncin ne a ranar Litinin, kafin wasan da kungiyar za ta yi tattaki zuwa gidan Empoli.
Hukuncin dai ya kai ta matsayi na bakwai daga matsayi na hudu a saman teburin gasar Seria A, wanda hakan zai hana ta samun damar shiga gasar Turai.
Tuni dai Napoli ta samu nasarar lashe kofin Seria A, kuma kafin yanke hukuncin na ranar Litinin, tana gaban Juve da maki 17.
Mai gabatar da kara na tarayya, Giuseppe Chiné ya nemi da a dakatar da jami’an kungiyar da ke da hannu a tuhumar na tsawon watanni takwas.
Hukuncin na nufin makin da Juventus ke da shi zai koma 58, inda za ta kasance a matsayi na shida.