Yusuf Shuaibu" />

An Rasa Naira Biliyan 645.15 A Bangaren Lantarki A 2020

Rashin Wutar Lantarki

Bincike ya nuna cewa, an rasa naira biliyan 645.15 a bangaren wutar lantarki a shekarar 2020, sakamakon raguwar karfin wutar lantarki na megawatt 44,068. An dai rasa wadannan makudan kudaden ne a bangaren wutar lantarki sakamakon rashi bayar da wutar lantarki akai-akai saboda matsalolin da ake samu na samarwa a bangaren. Bincike ya nuna cewa, an samu wannan matsala a bangaren wutar lantarki na tsawan wata 12, sakamakon rashin isasshen gas wanda zai rarraba wutar lantarkin.

Ma’aikatar wutar lantarki ta tarayya ta gabatar wa manema labarai takardar yawan kudaden da aka tafka a sara tun daga watan Junairu har zuwa watan Disambar shekarar 2020, takatdar tana dauke da yawan nairorin da aka tafka asaraga kowacce wata. An dai fi samun asara a watan Maris, wanda aka yi asarar kudaden shigan da ya kai na naira biliyan 65.55, yayain da aka samu karancin asara a watan Disamba na naira biliyan 25.55. Yawan kudaden da aka yi asara a watan Junairu da watan Fabrairu da watan Afrilu da watan Mayu da watan Yuni da kuma watan Yuli, ya kasance kamar haka, naira biliyan 56.41 da naira biliyan 54.96 da naira biliyan 64.64 da naira biliyan 61.6 da naira biliyan 61.77 da kuma naira biliyan 63.21.
Haka kuma, a cikin watan Agusta da watan Satumba da watan Oktoba da kuma watan Nuwamba, an tafka asarar kudaden shiga kamar haka, naira biliyan 62.92 da naira biliyan 45.99 da naira biliyan 52.58 da naira biliyan 29.97. An bayyana cewa, an samu raguwar karfin wutar lantarki a watan Junairu wanda ya kai na megawatt 3,791. A cikin watan Afrilu ne aka fi samun karancin wutar lantarki wanda ya aka sami na megawatt 4,489. Takardar da ke dauke da bayanan tafka asarar ya nuna yawan karancin wutar lantarkin a kowacce wata kamar haka , an samu karancin wutar lantarki a watan Fabrairu na 3,949, an samu na 4,406 a watan Maris, an sami na 4,290 a watan Mayu, an sami na 4,248 a watan Yuli. Sauran sun hada da, an sami na 4,229 a watan Ogusta, an sami na 3,194 a watan Satumba, an sami na 3,534a watan Oktoba, an sami 2,081, an samu na 1,717 a cikin watan Disamba.
Manema labarai sun bayyana cewa, daga cikin karancin wutar lantarkin wanda aka samu na watannin 12, an dai fi samun karancin wutar lantarki a cikin watan Ogusta.
Wannan asara na rasa kudade mai yawa daga kudaden shiga a bangaren wutar lantarki ya yi matukar raunata harkokin kasuwancin wanda ya shafi samar da kayayyaki da kamfanoni suke yi. Kamfanoni rarraba wutar lantarki sun yi korafin cewa, an samu wannan matsala a bangaren wutar lantarki ne sakamakon matsalolin rarraba wutar da aka saamu saboda karancin gas.
Kwamishina a sashen lasisi da ke cikin hukumar kula da wutar lantarki na kasa (NERC), Dafe Akpeneye ya bayyana wa manema labarai a Abuja cewa, idan ba a samu dai-daituwar farashin wutar lantarkin ba, to haka kasuwancin a bangaren wutar lantarki zai ci gaba da masun matsaloli.
Ya ce, “har yau kamfanonin rarraba wutar lantarkin ba su cimma matsaya a kan farashin wutar lantarki ba.
“A yanzu an rufe kofar zuba jari a bangaren rarraba wutar lantarki. wannan ne ya saka kowa yake saka farashin da ya ga dama, shi ya sa har yanzu ba mu fitar da kudadenmu ba.”
Akpeneye ya bayyana cewa, a yanzu haka hukumar kula da wutar lantarkin tana kokarin maganci matsalolin da bangaren wutar lantarkin fuskanta domin ci gaba da samun kudaden shiga masu yawa.
Ya ce, “idan aka sami dai-daituwar farashi, to za a samu kudaden haraji masu yawa a bangaren wutar lanntarki. Har yanzu akwai dinbi mutane masu yawa da suke sha’awar zuba jari a bangaran wutar lantarki a Nijeriya.
“Saboda ana samu gagarumar riba a bangaren wutar lantarkin Nijeriya. Amma a yanzu ana samun faduwa, babu kuwa wanda zai so ya zuba jari ya fadi. Idan ana samu nasarar magange matsaloli, to za a sami yawan masu zuba jari.”

Exit mobile version