A yau Litinin ne aka rufe gasar wasannin motsa jiki ta masu bukata ta musamman ta kasar Sin karo na 12, da gasar Olympics ajin rukunin mutanen masu bukata ta musamman karo na 9, a birnin Shenzhen na lardin Guangdong.
An gudanar da gasannin ne tsakanin ranakun 8 zuwa yau 15 ga watan Disamban bana, an kuma gudanar da rukunonin wasanni 46, inda jimillar ’yan wasa 7,824 daga tawagogi 34 suka yi rajistar fafatawa a gasannin.
A yayin gasannin, an karya matsayin bajimta 15 na duniya, da na kasar Sin 156. (Saminu Alhassan)
ADVERTISEMENT














