An yi garkuwa da wasu masu yi wa kasa hidima (NYSC) guda takwas a jihar Zamfara.
Wadanda aka sace sun fito ne daga garin Uyo na Jihar Akwa Ibom zuwa Jihar Sakkwato a cikin wata motar bas ta Kamfanin Sufurin Akwa Ibom (AKTC) domin yi wa kasa hidima na shekara daya.
- Harkar Tsaro Za Ta Bunkasa Nan Da Shekara Guda -Badaru
- Matar Aure Ta Kashe Dan Kishiyarta Mai Kwana 4 A Duniya A Bauchi
Wani babban jami’in kamfanin sufurin ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a ranar Talata.
A cewar majiyar, motar bas din tana dauke da mutane 11 da direban motar, amma uku daga ciki sun tsere yayin da aka yi awon gaba da guda takwas tare da direban.
“Sun bar nan (Uyo) ranar Juma’a, suka kwana a Abuja. A lokacin da suke kan hanyar zuwa Sakkwato ne aka yi garkuwa da su. ‘Yan sanda sun kwato bas din,” in ji jami’in.
Masu amfani da shafukan sada zumunta sun gano biyu daga cikin hotunan wadanda aka sace.
Wani ma’abocin Facebook, Malachy bless, ya bayyana daya daga cikin wadanda aka sace mai sunan Emmanuel Esudue, wanda ya kammala karatun aikin gona da injiniyan muhalli na Jami’ar jihar Akwa Ibom, ya ce tun ranar Alhamis ba a samun lambar wayar Esudue.
Wani ma’abocin Facebook Edidiong Richard ya bayyana cewa masu garkuwa da mutane sun tuntubi iyayen wata yarinya mai suna Betty Udofia inda suka bukaci a biya su miliyan hudu a matsayin kudin fansa.