Wani rahoto da kamfanin Beacon Consulting da ke nazarin tsaro a yankin Afirka ta Yamma da yankin Sahel ya fitar, ya nuna cewa a watan Yulin da ya gabata, an samu karuwar satar mutane domin kudin fansa a Nijeriya idan aka kwatanta da watan Yuni.
Shugaban kamfanin, Dakta Kabir Adamu, ya shaida wa BBC cewa, a watan Yuli kadai an sace kusan mutane 1,035, amma kuma an samu ragi na adadin wadanda ake kashewa.
- Kwanaki 11 Da Hawa Kujerar Mulki, Mataimakin Shugaban Iran Ya Yi Murabus
- NIS Ta Fara Binciken Wata Mata Da Ta Yayyaga Fasfonta A Filin Jiragen Sama Na Legas
Ya ce, bisa ga mizanin da suke aunawa, a watan Yunin 2024 an sace mutum 468, yayin da a watan Yuli kuma aka sace mutum 1,035.
Ya ce, “Idan aka auna, za a ga kari aka samu wanda ya rubanya adadin na baya ma, amma dangane da mace-mace kuwa, an dan samu ragi, don ba wani mai yawa bane.”
Shugaban kamfanin na Beacon Consulting, ya ce da suka yi nazari, sun gano cewa akwai abubuwan da suka janyo hakan, muhimman kuwa su ne tasirin da tabarbarewar tattalin arziki ke yi ga bangaren tsaro.
Ya ce, “Abu na biyu kuwa shi ne siyasa, wato ‘yan siyasa na amfani da matsalar tsaro suna kokarin cimma burinsu, sai kuma abu na karshe shi ne matsalar zamantakewa a tsakanin jama’a kamar shaye-shaye da suka yi tasiri a bangaren tsaro.”
Har wa yau, ya ce wani abu da suka lura da shi ne, masu satar mutanen sun sauya yadda suke karbar kudin fansa.
Ya ce, “A da su kan bukaci a ba su kudade masu yawa, amma a yanzu sun sauya salo saboda yanzu jimillar kudade suke bukta, ma’ana idan suka hada mutane da yawa, sai su bukaci a ba su kudinsu a tare.”