An gano wani yunkuri a cikin jam’iyyar adawa ta PDP na barin mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, Iliya Damagum ya ci gba da rike mukaminsa har na tsawon wa’adin Dakta Iyorchia Ayu ya kare a 2025.
Duk da cewa tun da farko an tsayar da taron kwamitin zartarwa na jam’iyyar zuwa ranar 28 ga watan Nuwamba, taron gwamnonin jam’iyyar PDP da suka gudanar a Bauchi a karshen mako sun nuna cewa a dage zaben zuwa wani lokaci a cikin watan Fabrairun 2025, domin samun damar jam’iyyar ta warware matsalarta na ciki gida.
- Yadda Gwamnonin PDP Suka Ceto Damagun Daga Kora
- Online Payday Loans In Conrad, Montana Mt From Direct Lenders
Sai dai wasu majiyoyi sun shaida cewa matakin sauya shekar na kwamitin zartarwar nasara ce ga masu neman Damagum ya ci gaba da rike mukamin har zuwa karshen shekarar 2025.
Wata majiya ta ce tuni aka samu rabuwar kawuna, inda bangarori biyu suka kunno kai a cikin jam’iyyar PDP. Yayin da aka ce wani bangare wanda ya hada da wasu gwamnoni da masu ruwa da tsaki na kokarin ganin an tsawaita wa’adin zama a Damagum, dayan bangaren wanda kuma ya kunshi wasu gwamnoni da wasu masu fada ji na jam’iyyar suna aiki tukuru wajen ganin an zabi wani shugaban jam’iyya, wanda zai tabbatar da bin tsarin mulkin jam’iyyar kamar yadda aka saba a baya.
Damagum ya fito ne daga shiyyar arewa maso gabas, tun farko an zabe shi a matsayin mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa reshen arewa kafin ya hau kujerar mukaddashin shugaban jam’iyyar na kasa, bayan tsige Dakta Iyorchia Ayu.
Kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya nuna cewa dole ne wanda zai maye gurbin Ayu ya fito daga yanki da da shi, amma makirci ya mamaye jam’iyyar, wanda ya tabbatar da tsawaita jinkirin aiwatar da maye gurbin.
Wani shiri na samar da wanda zai maye gurbinsa daga arewa ta tsakiya ya ci karo da matsaloli bayan dage babban taron kwamitin zartarwa na jam’iyya da aka yi akai-akai. Taron na karshe da kwamitin zartarwa na jam’iyyar ta gudanar a ranar 18 ga watan Afrilu, an sanya ranar 15 ga watan Agusta domin gudanar da zaben shugaban jam’iyyar karo na 99, amma an dage taron da farko zuwa ranar 24 ga watan Oktoba, sannan zuwa ranar 28 ga watan Nuwamba, wanda a yanzu kungiyar gwamnonin na jam’iyyar ta kara dagawa.
Bincike ya nuna cewa yayin da masu neman maye gurbin Damagum ke neman wanda zai iya karbar ragamar mulki nan take, masu goyon bayan ci gaba da aikinsa a ofishin sun yi ta aiki a asirce kan yadda zai karasa sauran wa’adin Ayu, sannan kuma a sake zabensa a karo na biyu a 2025 don samun cikakken wa’adinsa.