Bayanan da hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta kasa na makin data amince da shi a hukumunce wanda idan aka same shi za a iya shiga dukwata babbar makaranta,wato kati mafi karanci da ake bukata a shekarar karatu ta 2024/2025 yasa an samu rarrabuwar kai daga masana ailimi,dalibai Iyaye,da kuma masu ruwa da tsaki a Nijeriya.
A taron hukumar JAMB 2025 wato tsarin da ake da shi wanda aka yi ranar Talata Abuja, Hukumar tace, kamar yadda hukumar ta hada kai da makarantiu aka kuma amince da maki, 150 a matsayin mafi karancin maki wanda za a iya samun shiga Jami’oin Nijeriya, 100 ga makarantun fasaha da Kwalejojin ilimi, yayin da 140 na Kwalejojin kimiyyar Nas- Nas.
- Philippines Na Zama Tushen Tashin Hankali A Tekun Kudancin Kasar Sin
- Dillalai Sun Rage Farashin Man Fetur A Nijeriya
Yayin da shi matakin yayi la’akari da shekarun da suka gabata wato na yadda ake ba su makarantun damar daukar mataki na irinmakin da suke bukata,yayin da su kuma ‘yan gaza- gani abin yayi kasa sosai,yin hakan shi yasa ake ta maganganu kan irin nagartar shi ilimin,da kuma irin yadda ilimin manyan makarantu zai iya kasancewa nan gaba a Nijeriya.
Rajistaran JAMB Farfesa. Ishak Oloyede, ya bayyana cewa dalilin da yasa aka dauki matakin an yanke hukuncine da yardar kowa, saboda la’akarin da aka yi irn halin da lamarin ilimi yake ciki a Nijeriya.
Ya ci gaba da bayanin yayin da maganar makin da aka amince mafi karanci domin samun damar shiga, kowace makaranta na iya ko nada damar su kara ko ta kara irin makin da take bukata, wannan kuma ya danganta ne kan irin yadda dalibai suke rububin zuwa makaranta na irin kwasa- kwasan da take da su.
“Shi wannan tsarin yana nuanwa a fili babu boye- boye na irin halin da lamarin ilimi yake a Nijeriya, da kuma bukatar a rika btafiya da lamarin cancanta, adalci, sai kuma irin yadda ita Jami’ar ko makarantar take son makin data kaiyade ya kasance,duk da haka suna da halin su sa irin makin da suke so.”
Ya kara yin bayanin da yake nuna ita hukumar JAMB babban aikinta shi ne ta kasance wanda take tsawatawa kan lamarin daya shafi neman shiga babbar makaranta, domin ta tabbar da ana bin dokokin yin hakan,wato lura yadda jami’ar,rika yin adalci, a kuma rika yin abu ba wata mina- mina.
Shi ma da yake na shi jawabin lokacin taron, Ministan ilimi, Dakta Maruf Alausa, ya yi kira da makarantun da babu wani wanda aka maida shiu saniyar ware saboda yadda Iyayen shi suke idan aka yi la’akari da al’amarin zamantakwa da tattalin arziki,akwai kuma ko su makarantun suna yin abubuwansu ba wata rufa- rufa. Bugu da kari dole su makarantu ya kasance suna da nasu tsarin kamar dai kuma yadda tsarin na kasa yake.”
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp