Connect with us

LABARAI

An Shawarci Gwamnatin Jihar Neja Kan Gudanar Da Aiyyuka

Published

on

An yi kira ga gwamnatin Neja da ta yi kokarin cika alkawurran da aka yi wa jama’a lokacin yakin neman zabe ga jama’a, duba da irin halin da ake ciki yanzu gwamnatin kamar ta rasa alkibla duk da irin kudaden da ta ke samu daga aljihun gwamnatin tarayya. Tsohon dan takarar kujerar gwamnan jihar a inuwar APC, Sanata Ibrahim Musa ne ya yi kiran a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Kontagora.
Sanatan ya ci gaba da cewar batun cewar gwamna Abubakar Sani Bello bai yi wa kowa alkawari ba a lokacin yakin neman zabe ba gaskiya ba ne, domin duk wanda yaci zabe a inuwar APC yasan abinda yasa talakawa suka zabe shi, don haka ya kamata ya fito dan cika alkawurran da aka yiwa jama’a.
Tsohon sanatan ya ci gaba da cewar yanzu aikin hanyar Kontagora zuwa Rijau ya gagara, aikin hanyar Kontagora zuwa Bangi ya gagara, ga aikin hanyar Mokwa zuwa Bargu wanda duk hakki ne na gwamnatin jiha ta tabbatar da ta yi amma har yanzu shiru kamar an shuka dusa. APC tayi alkawalin kawo canji da inganta rayuwar al’umma amma mu a jihar Neja babu komai kamar ma ba gwamnatin da talakawa suka zaba ba.
Mu a yankin Neja ta Arewa, ba mu taba yin wata jam’iyya wadda ba ta Shugaba Muhammadu Buhari ba, wanda shi kanshi shaida ne akan hakan, domin in za a lissafa yankunan da shugaban kasa ke da magoya baya, to lallai muna sahun farko amma shekaru ukun APC akan karagar mulki tun daga kan rabon mukamai har zuwa aikin cigaban kasa to muna baya.
Ya kamata tunda gwamna ya fito daga yankin nan ne ya nemo ‘yan siyasa na gaskiya wadanda suke gwagwarmaya har kafa wannan gwamnati da su laluba mai hanyar da za ta fitar da shi, don wadanda ya sanya a gaba ba zasu iya kai shi gaci ba.
Dangane da kujerar da tsohon mataimakin gwamnan Neja, Ahmed Musa Ibeto ya ajiye kuwa, sanatan yace mun san a rina ai, ya fado ne a tafiyar daga sama kuma sai aka yi azarbabin bashi mukami alhalin akwai wadanda suka fi shi cancanta, tau shugaban kasa bai taka tsantsan ba ‘yar gidan jiya za a koma domin wanda gwamnatin jiha ke kokarin aika sunansa ba abinda zai iya tabukawa.
Sanata Ibrahim Musa ya tabbatar wa magoya bayansa cewar yana nan daram a jam’iyyar APC kuma da shi za a sake sakawa a zaben gwamna na 2019 mai zuwa, dan haka ya jawo hankalin magoya bayansa da su zama masu bin doka da oda, duk lokacin hukumar zabe ta bada damar fara yakin neman zabe su fito a fara aiki amma yanzu maganar zabe ko kafa fastoci lokaci bai yi ba tukin na.
Advertisement

labarai