Wata ƙungiya da ke kira a zauna lafiya mai suna Arewa Social Contract Initiative ta yi kira ga tsohon Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero da ya fita daga jihar domin samunr da zaman lafiya.
A wani taron manema labarai da ya gudana a Kano yau Lahadi, shugaban ƙungiyar Kwamared Sani M. Darma ya ce komowar Sarki Aminu da yunƙurin kwatar karagar mulki zai haifar da tashin hankali da hargitsi. Don haka ne ya ba da shawara ga Sarki Aminu Ado da ya koma wata jihar ko da kuwa yana jiran hukuncin kotu.
- Jami’an Tsaro Na Ganawar Sirri Da Abba Da Sarki Sanusi II A Fadar Kano
- Ina Nan A Matsayin Sarkin Kano, Har Sai Na Ga Umarnin Kotun – Sanusi II
Darma ya ƙara da cewa, sai da Sarki Aminu Ado ya amince da tsige shi amma daga baya sojojin gwamnatin tarayya suka tilastawa Sarki Aminu komowa, lamarin da ya ke yunƙurin ta da zaune tsaye a Kano.
Ya kwatanta lokacin da Sarki Sanusi Lamido Sanusi hakan ta faru a kansa, wanda ya tafi lami lafiya bayan an sauke shi daga karagar mulki, inda ya nuna mutuntaka don a samu zaman lafiya.
Da yake bayyana goyon bayansa ga Mai Martaba Sarki Sanusi, Darma ya ce,’ dawowar Sarki Sunusi cika alkawarin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi ne lokacin yaƙin neman zabensa, wanda ya samu amincewar jama’a.
Don haka ne ya shawarci Sarki Aminu da ya yarda da lamarin, ya bar Kano, ya kuma taya sabon Sarkin murna don ganin an samu zaman lafiya a jihar.