Akwai damuwa da ake nunawa dangane da jinkirin biyan ‘yan kwangila kudaden ayyukansu da gwamnatin tarayya ke yi.
Shugaban kwamitin da ido da tantancewa na majalisar wakilai, Obi Aguocha, shi ne ya bijiro da damuwowin a kwanakin baya. Ya nemi gwamnatin Nijeriya da ta duba lamarin biyan ‘yan kwangila kudadensu da suke bi tun shekarar da ta gabata.
- Sin Ta Wanzar Da Ruhin Juriya Ta Hanyar Yakar Tafarkin Murdiya
- Dakarun PLA Sun Gudanar Da Sintiri A Yankin Tekun Kudancin Sin
A farkon watan Yunin 2025, dan majalisar daga Jihar Bauchi, Sanata Abdul Ahmed Ningi, ya nuna damuwa kan rashin biyan ‘yan kwangila kudadensu da gwamnatin tarayya ta kasa biya tun 2024. Ningi a gaban majalisar ya nemi a gaggauta gudanar da bincike kan lamarin.
Sai dai a martanin gwamantin tarayya ta ofishin OAGF ta nuna aniyarta na fara biyan ‘yan kwangilan. Sai dai ba a cika alkawarin a kan lokaci ba.
Lamarin ya ci gaba da zaman damuwa da abun korafi a tsakanin masu ruwa da tsaki da suke nuna hakan zai shafi tattalin arziki.
Da yake ganawa da ‘yan jarida a ranar Litinin, tsohon shugaban kungiyar masu tsara gidaje a Nijeriya, Aliyu Wammako, ya ce, rashin biyan ‘yan kwangila kudadensu na shafan tattalin arziki sosai.
Ya bukaci gwamnatin tarayya da ka da ta tsaya bata wani lokaci ta kama biyan ‘yan kwangila kudadensu da hakan zGwamnatin tarayyar Nijeriya ta kaddamar da wani kwamiti da zai tattauna batun basussukan da suka dabaibaye harkokin jakadancin Nijeriya a kasashen ketare.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin kasashen waje, Kimiebi I. Ebienfa, shi ne ya shaida hakan ya cikin sanarwar da ya fitar a ranar Litinin a Abuja.
Ebienfa ya ce an dauki matakin ne domin tabbatar da cewa an yi amfani da kudaden da aka tura domin gudanar da ayyukan jakadanci cikin gaskiya da kuma kula da su cikin tsanaki bisa tsarin tafiyar da harkokin kudi na gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Ya ce ma’aikatar ta kuma tuntubi ofishin akanta janar na kasa da min ta nemi maido da gibin kudaden da aka ware wa harkokin jakadancin da aka samu cikin kasafin 2024 sakamakon musayar kudade daga sabbin tsare-tsaren kudade da daidaita farashin musayar kudaden.
Idan za a tuna dai gwamnatin tarayya ta amince kan cewa akwai kalubalen kudade da na ayyuka da suke shafan ayyukan diflomasiyya da harkokin jakadancin a kasashen waje.
Ya ce, hatta ofishin jakadancin Nijeriya da suke ketare ba su fita daga matsalolin tattalin arziki da ake fuskanta a cikin gida Nijeriya ba.
“Halin da ake ciki kan hada-hadar kudi da ke fuskantar ofishin jakadanci ya samo asali ne daga gazawar kasafin kudi a tsawon shekaru, wanda ya haifar da cikas a cikin kasafi, kuma ya yi tasiri sosai wajen gudanar da ayyuka da yawa na ofisoshin jakadanci a kasashen waje da kuma karfinsu na aiwatar da muhimman ayyukan diflomasiyya da na ofishin jakadanci yadda ya kamata.”
Sanarwar ta ce “Gwamnatin tarayya ta yi bakin kokarinta wajen ganin ta maye gurbin wasu manyan jakadu, wadanda aka musu kiranye a ranar 1 ga Satumba, 2023.”
ai yi tasiri a dukkanin bangarorin tattalin arziki.
“Rashin biyan ‘yan kwangila kudadensu da gwamnatin tarayya ke ci gaba da yi babban matsala ce da ke shafan kasar baki daya. Saboda musayar kudade tsakanin ‘yan kwangila, leburori, da kwararru ne tushen tattalin arzikin kasa,” in ji shi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp