Wasu ‘yan bindiga sun kai hari hedikwatar Karamar Hukumar Zurmi ta Jihar Zamfara, inda suka yi ta harbe-harbe.
Wani mazaunin garin Mustapha Zurmi ya shaida wa Leadership Hausa, cewa galibin mazauna sun tsere zuwa cikin daji domin tsira da rayukansu.
- NLC Ta Yi Barazanar Sake Shiga Yajin Aiki
- MDD Za Ta Sake Shirya Taron Kada Kuri’a Kan Tsagaita Wuta A Gaza
A cewarsa wasu kuma sun kulle gidajensu don gudun kada ‘yan ta’addan su kashe su ko kuma su yi garkuwa da su.
Zurmi ya ci gaba da cewa, jami’an sojin da aka tura garin domin ceto rayuka da dukiyoyin jama’a ba su isa su shawo kan lamarin ba.
Ya yi nuni da cewar ‘yan bindigar na ci gaba da hare-hare a yankin.
Ya kara da cewa babu wanda zai iya tantance adadin mutanen da aka kashe ko aka sace.
“Dukkanmu muna tsoron kada ’yan ta’addan su kashe mu ko kuma su yi garkuwa da mu. Muna fuskantar babban kalubalen tsaro a yankin saboda jami’an sojin da aka tura domin yakar ‘yan bindigar ba su da yawa,” in ji shi.
Kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ’yansandan jihar, ASP Yazid Abdulahi, ya ci tura saboda ba ya amsa kiran waya.