Wata kotun shari’ar Musulunci a Jihar Kano, ta bayar da umarnin ci gaba da tsare wani matashi dan shekara 28, Badamasi Abubakar, a gidan yari, bayan da ya amsa laifin cire wa wata mata mayafi ba tare da izininta ba a ranar Alhamis.
Abubakar, wanda mazaunin unguwar Hotoron Dan Marke ne, a Kano, ya amsa laifinsa na cin zarafin matar.
- ‘Yan Bindiga Sun Kona Ofishin ‘Yan Sanda Da Gidaje a Zamfara
- Kwankwaso Da Fayose Sun Ziyarci Wike A Fatakwal
Alkalin kotun, Ismail Muhammed-Ahmed, ya dage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 27 ga watan Yuli domin yanke masa hukunci.
Tun da farko, mai shigar da kara, Sifeto Abdul Wada, ya shaida wa kotun cewa Summaiya Abdul da ke unguwar Hotoron Dan Marke, ta kai karar ofishin ‘yan sanda na Hotoro a ranar 21 ga watan Yuni.
Mai gabatar da kara ya ce mai shigar da kara ta ce da misalin karfe 4 na yamma, wanda ake karar ya yaye mata mayafi ba tare da izininta ba, kuma da ta yi masa magana kawai sai ya wanke ta da mari.
Wada ya ce laifin ya saba da sashe na 165 da 166 na kundin laifuffuka na Jihar Kano na shekarar 2004.