Ana tuhumar tsohon Firaministan Mali, Choguel Kokalla Maiga, da zargin almubazzaranci da dukiyar jama’a da kuma yin takardun bogi.
An cafke shi ne a ranar Talata, 19 ga watan Agusta, a lokacin da gwamnatin mulkin sojin Mali ke ci gaba da matsa wa ‘yan siyasa da ke sukar gwamnati.
- An Gano Karin Gawarwaki 3 Da Jirgin Ruwa Ya Kife Da Fasinjoji 26 A Sokoto
- Ronaldo Ya Samu Kyakkyawar Tarba A Hong Kong
Maiga ya riƙe muƙamin firaminista daga shekarar 2021 har zuwa ƙarshen shekarar 2024, lokacin da aka tsige shi daga mukamin.
A baya ya sha sukar gwamnatin sojin da ta jinkirta komawa mulkin farar hula.
Lauyansa, Cheick Oumar Konaré, ya ce wannan tuhuma ba komai ba ce illa bita-da-ƙulli irin na siyasa.
Kamen ya zo ne jim kaÉ—an bayan da aka tsare wasu sojoji sama da 50 da wani É—an Faransa, bisa zargin shirin tada zaune tsaye.
Shugaban ƙasar, Janar Assimi Goïta, wanda ya karɓi mulki a 2020, ya amince da wata doka da ke ba shi damar ci gaba da mulki ba tare da iyaka ba, yana mai cewa hakan don yaƙi da masu tayar da ƙayar baya ne a ƙasar.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp