Zubairu T M Lawal" />

An Tuna Da Ranar Da Aka Yi Wa Yahudawa Kisan Kiyashi A Duniya

hare-haren

epa06071624 UN Secretary-General Antonio Guterres informs the media that the conference on Cyprus under the auspices of the United Nations (UN) is closed without any agreement, in Crans-Montana, Switzerland, 07 July 2017, after diplomatic efforts to reunite the island in the eastern Mediterranean Sea. EPA/SALVATORE DI NOLFI

Majalisar Dinkin Duniya, ta gabatar da taron tunawa da kisan kiyashi da aka yi wa Yahudawa. Da yake mika sakon Majalisar Dinkin Duniya, Sakatare Janar Antonio Guterres ya ce; “Yau rana ce da Duniya take bikin tunawa da kisan kiyashi da aka yi wa al’umman Yahudawa kimanin miliyan shida a Duniya.
Ya ce; miliyan shida din nan wadanda alkaluma suka kididdige kenan, ban da wadanda ba a gani ba. Bikin ya gudana ne a ranar 27 da 28 na watan Janairu a duniya, inda a nan kasar ma aka gudanar da shi a madadin Ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke Abuja da Lagos.
Ofishin yada Labarai na al’amurar Majalisar Dinkin Duniya ya kasance mai kula da al’amuran bukukuwan, inda aka raba sakon Sakatare Janar da ya karanta wa Duniya a wannan ranar.
Ya ce; bayan kisan gillar da aka yi wa yahudawan, sun samu tallafi daga gamayyar yankin Turai da na Amurka. Ana samun tunawa da ire-iren wadanan kalamai daga cibiyar nazari ta Nazi, wanda suka tsakulo wannan tarihin.
Kungiyoyi da dama suna nuna jimami game da abubuwan da suka faru a irin wannan lokacin.
Kuma ana samun kungiyoyin da ke tausayawa da nuna jimami har ma da kungiyar Musulmai ta Duniya suna nuna bakin cikin su.
Wannan ranace da za mu tuna mu kuma nuna jimami mu tausaya saboda abin da ya faru tarihi ba zai manta da shi ba a rayuwa.

Exit mobile version