Sanatan da ke wakiltar Kudu maso Gabashin Borno, Ali Ndume, ya bayyana damuwarsa game da karuwar rashin jin dadi a cikin jam’iyyar APC, yana mai cewa wasu daga cikin manyan shugabannin jam’iyyar suna jin cewa an bar su a gefe a karkashin mulkin Shugaba Bola Tinubu.
Ndume ya bayyana wannan ne lokacin da yake wata hira a shahararren shirin siyasa mai suna ‘Politics Today’ na gidan Talabijin din Channels a ranar Juma’a. Sanatan ya nuna bakin cikin sa game da yadda wasu manyan jami’an jam’iyyar ba sa samun damar tattaunawa ko samun hulda da gwamnatin tarayya.
- Da Gangan Aka Rikirkita Tsarin Zaben Nijeriya Domin A Samu Damar Yin Magudi – Sanata Ndume
- Ficewar Kasar Nijar Daga Rundunar Hadin Gwiwa Ta Kasa Da Kasa Barazana Ce Ga Tsaro -Hedikwatar Tsaro
“Fiye da shekara guda cikin mulkin, da dama suna jin an barsu a gefe. Kamar El-Rufai, ya bayar da dalilin cewa APC ta bar shi, haka ma wasu da dama,” in ji Ndume, yana nuni da tsohon gwamnan Jihar Kaduna wanda ya bar APC domin shiga jam’iyyar Social Democratic (SDP).
Ndume ya kara da cewa gwamnati tana nuna rashin sha’awar magance damuwar da yan jam’iyyar suka bayyana. “Da dama ba su da damar shiga gwamnati. Na fada haka wasu lokuta, amma bai yi wani abu ba. Maimakon haka, suna komawa cikin jaridu suna zagin mai kawo sakon maimakon duba sakon,” ya kara da cewa.
A cikin wata hira da yayi a Arise News TV a ranar Litinin, Sanatan Ndume ya kuma zargi Shugaba Tinubu da nuna fifiko ga wasu mutane a cikin mukaman gwamnati.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp