Muhammad Sani Chinade" />

An Yaba Wa Gwamnan Yobe Kan Tallafa Wa Kananan ‘Yan Kasuwa

An bayyana cewar, matakin da gwamna Mai Mala na Jihar Yobe ke dauka na bada tallafi ga masu sana’o’i don ganin an kawo al’umma kusa da gwamnati, lamari ne da ke da matukar muhimmanci kuma ya yi dai-dai.

Bayanin hakan dai ya fito me daga bakin wani mai sana’ar sayar da shayi, Malam Musa Muhammad da ke sana’ar sayar da shayi a cikin tashar motar Damaturu a cikin tattaunawarsu da wakilinmu bisa  ga matakin da gwamnan ke dauka wajen rarraba Karin jari ga masu kananan sana’o’i a cikin garin Damaturu fadar Jihar. Malam Musa Muhammad ya kara da cewar, yana zaman sa said kwatsam rannan ya ga wata tawaga ta same shi aka ce masa ga sako daga gwamnan cewar, a bashi kudi Naira dubu Hamsin don ya kara jari.

A cewarsa a rayuwarsa bai taba tsammanin hakan ba, lamarin ya yi matukar ba shi mamaki da al’ajabi ganin cewar, shi ba Sanin gwamnan ya yi ba kuma babu wata alaka.

Ya kara da cewar, daga bisani sai ya ji cewar, ashe wannan abin alheri da gwamnan ya aiko masa ba shi kadai bane, akwai sauran masu sana’o’i irin ya nasa da suma suka amfana.

Don haka ya yi fatan alheri ga gwamnan kasancewar a Sanin tunda ake zaben gwamna a Jihar tasu ta Yobe ba su taba gwamnan da ya taba irin haka ba.
Ya kuma roki gwamnan da ya fadada irin wannan aiki na alheri ya karade dukkan fadin Jihar, duk da cewar nasan gwamnan zai yi hakan.

 

 

Exit mobile version