Tsohon ɗan gaban wasan Manchester United, Wayne Rooney, ya ce an yi barazanar kashe lokacin da ya bar Everton ya koma Manchester United.
Rooney ya koma United yana da shekaru 18 a shekarar 2004, inda ya sanya hannu kan yarjejeniya mai darajar Yuro miliyan 27, bayan ya ƙi sabunta kwantiraginsa a Everton.
- Waiwaye Adon Tafiya: Manyan Nasarorin Da Aka Cimma A Dangantakar Kasashen Afirka Da Sin A 2025
- Kotu Ta Umarci EFCC Ta Biya Wani Ƴan Kasuwar Kano Miliyan 5, Ta Nemi Afuwar Su
Rooney, ya ce wasu magoya bayan Everton sun fusata sosai da barinsa kulob ɗin, lamarin da ya kai ga yi masa barazanar kisa.
Ya bayyana hakan a cikin shirinsa na The Wayne Rooney Show, inda ya ce har ma an yi wa gidan iyayensa da na budurwarsa feshin baƙin fenti.
Ya ƙara da cewa barin Everton abu ne mai wahala a wancan lokacin saboda Manchester United na saman makiyansj irin su Manchester City da Liverpool.
Amma duk da haka, ya ce ya dage domin ya san abin da yake nema da kuma burinsa a ƙwallon ƙafa.
Rooney ya kuma bayyana cewa a lokacin da ya koma United, babu yawaitar kafafen sada zumunta kamar yanzu, amma sunansa ya yaɗu sosai a jaridun gida.
Ya ce hakan ya sa a lokacin matasa ‘yan wasa kan fuskanci matsin lamba sosai, saboda mutane suna hukunta su ko da sun yi daidai ko ba daidai ba.
Ya ce a irin wannan lokaci ake buƙatar abokai da waɗanda ke tare da kai domin samun ƙwarin gwiwa da ci gaba.














