Ofishin jakadancin Sin dake Zimbabwe, ya gudanar da bikin cika shekaru 60 da fara tura tawagar jami’an lafiya na kasar Sin zuwa ketare, tare da maraba da tawaga ta 20 na jami’an lafiya da Sin ta tura kasar a ran 8 ga watan.
Haka kuma, bikin ya taya tawaga ta 19 ta jami’an lafiya ta kasar Sin, murnar kammala aikinsu na shekara 1 a kasar, cikin nasara.
Tun bayan da Sin ta tura tawaga ta farko ta jami’an lafiya zuwa kasar Algeria a 1963, kawo yanzu, ta tura jimilar jami’an lafiya 30,000, wadanda suka bada kulawar lafiya ga mutane miliyan 290 a kasashe da yankuna 76. Yanzu haka, tawagar jami’an lafiya na kasar Sin na aiki a birane 115 a kasashe 56 a fadin duniya.
Tun daga shekarar 1985 zuwa yanzu, kasar Sin ta tura tawagogin jami’an lafiya 20 zuwa kasar Zimbabwe. Kuma cikin shekarar da ta gabata, tawaga ta 19 ta yi aiki bisa hadin gwiwa da ma’aikatar lafiya ta kasar da sassa masu ruwa da tsaki, wajen samar da kiwon lafiya ga al’ummar Zimbabwe.
Da yake jawabi yayin bikin, mataimakin shugaban kasar Zimbabwe kuma ministan lafiya na kasar, Constantino Chiwenga, ya yaba da rawar da kasar da Sin da ma jami’an lafiyar suka taka wajen yaki da annobar COVID-19 a kasar. Yana mai cewa, kashin farko na alluran riga kafin cutar da ya shiga kasar a watan Fabrerun 2021, gudunmawa ce daga gwamnatin kasar Sin, lamarin da ya kaddamar da ganganmin riga kafi cikin nasara a kasar, inda zuwa yanzu ta yi wa kaso 60.8 na jama’arta riga kafi.
Sannan aka yi bikin mika aiki daga tawagar likitoci ta kasar Sin dake kasar Zimbabwe karo na 19 zuwa ta 20 a birnin Harare, inda mukaddashin jakadan Sin dake Zimbabwe Cheng Yan da mataimakin shugaban Zimbabwe kuma ministan kiwon lafiyar kasar Constantino Chiwenga suka halarci bikin.
A yayin bikin, a madadin gwamnatin Zimbabwe, minista Chiwenga ya ba da lambar yabo ga hukumar kiwon lafiya ta lardin Hunan na kasar Sin, wadda ta dauki nauyin tura tawagogin likitoci ga Zimbabwe cikin tsawon shekaru 38 da suka gabata. (Fa’iza Mustapha, Zainab Zhang)